Bishop na ɗarikar Kiristoci ta Katolika na yankin Sakkwato kuma Shugaban Jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu da ke Igbariam, Jihar Anambra, Rabaran Dakta Matthew Kukah, ya buƙaci ’yan Nijeriya da su daina kiran sa Bahaushe.
Kukah ya ƙara da cewa shi cikakken ɗan Nijeriya ne, amma ba Bahaushe ba ne asali, duk da yadda ake yawan kiran sa haka duk inda ya je.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a bikin yaye ɗalibai karo na 16 na jami’ar, wanda aka gudanar a babban ɗakin taro na jami’ar a ranar Asabar.
Ya shawarci ɗaliban da suka kammala karatu da su kasance masu kyawawan ɗabi’u ga iyayen su, al’ummar jami’a, Jihar Anambra, yankin Kudu-maso-gabas da Nijeriya baki ɗaya.
Sabon Shugaban ya yaba wa gwamnatin jihar kan gagarumin jarin da take zubawa a fannin ilimi, yana mai cewa a ƙididdiga, “Jihar Anambra na taka rawa sosai a harkar ilimi a cikin jihohi 36.”
Ya ce, “Ni cikakken ɗan Nijeriya ne daga Anchuna, masarautar Ikulu a Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna, amma ba Bahaushe ba ne asali. Ya kamata ’yan Nijeriya su daina kira na Bahaushe.
“A matsayi na na sabon Shugaban wannan jami’a, ba wai kawai za mu yi ƙoƙarin cimma manufofin jami’ar ba ne, har ma za mu ɗora kan su.”
Ya gode wa Gwamnan jihar, Chukwuma Soludo, bisa naɗa shi Shugaba na jami’ar.
Gwamnan jihar ne ya naɗa shi a matsayin Shugaban jami’ar a yayin bikin.
Da yake jawabi, gwamnan Jihar Anambra ya bayyana farin cikin sa yayin da yake sanya wa Kukah kayan matsayin sabon Shugaban jami’ar, yana mai bayyana gamsuwa da cewa hikimar sa da gogewar sa da shugabancin sa na ɗabi’a za su ƙara ƙarfafa hangen nesa da martabar jami’ar.
Soludo ya ce, “Babban abin alfahari ne gare ni kasancewa a bikin yaye ɗalibai karo na 16 na Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu University a matsayi na na babban baƙo ga wannan babbar cibiya.
“Bikin ya kasance bikin yabon ƙwazo, aiki tuƙuru da ƙarfin ingantaccen ilimi. Haka kuma ya tuna mana muhimmiyar rawar da jami’o’i suke takawa wajen horar da ƙwararrun ma’aikata, gina ɗabi’a, bunƙasa ilimi da shirya matasa su bayar da gudunmawa mai amfani ga al’umma.
“Na yi matuƙar farin ciki musamman wajen sanya wa Bishop na Katolika na Sokoto, Mai Girma Rabaran Dokta Matthew Hassan Kukah, kayan matsayin sabon Shugaban Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu University.
“Ina da yaƙinin cewa hikimar sa, gogewar sa da kyakkyawan shugabancin sa za su ƙara ƙarfafa hangen nesa da martabar jami’ar.
“Domin karrama gagarumar nasarar ilimi, na bayyana kyautar kuɗi ta naira miliyan 4 ga Somtochukwu Augustus Ume daga sashen tattalin arziki, wanda ya zama ɗalibin da ya fi kowa sakamako a bikin yaye ɗalibai na 16 na COOU da CGPA mai ban mamaki na 4.85 cikin 5.0.
“Haka kuma na ba da tallafin karatu ga ɗalibai 37 da suka kammala da daraja ta first class domin tallafa musu su ci gaba da karatun digiri na gaba har zuwa mataki mafi girma a kowace jami’ar gwamnati da suka zaɓa.”
Ya kuma buƙaci jami’ar ta ci gaba da mayar da hankali wajen samar da masu warware matsaloli maimakon masu kirga bayanai kawai.
“Cibiyoyin mu na ilimi mai zurfi dole su wuce bayar da takardun shaida; ya kamata su samar da masu ƙirƙire-ƙirƙire, masu kawo mafita, waɗanda za su iya gogayya a duniya, waɗanda za su iya fuskantar ƙalubalen zamanin mu.
“Ga ɗaliban da suka kammala, na buƙace su da su yi amfani da wannan dama su zama fitilun bege, masu tunani na sauyi, kuma wakilan canji a cikin al’umma. Makoma mallakar waɗanda suka shirya jagoranci da jarumtaka da ƙirƙire-ƙirƙire da manufa take,” inji shi.






