A yau babu wani yare a faɗin Afrika da ya kai Hausa yawan masu amfani da shi. Sannan kuma ƙabilar Hausawa a Nijeriya babu wata ƙabila mai tarihi da tasirin ta a shekarun baya. Hausawa sun laƙume yaruka da ƙabilu masu yawa. Wannan tasiri kuma ya faro tun kafin zuwan Musulunci ƙasar Hausa. Menene sirrin?
Akwai dalilai da dama, amma a fahimta ta shi ne abubuwa kamar haka: kasancewa Hausawa na da tsohon tarihi na tsarin zamantakewa da mulki, sannan da al’ada mai tagomashi da kuma karɓar baƙi daga ko’ina.
Wannan halayya ta karɓar baƙi ita ce mafi tasiri wajen yaɗuwar Hausa da al’adun Hausawa. Bahaushe ne za ka zo ƙasar sa bai san daga ina kake ba, ya ba ka masauki, ya ba ka sana’a, ya ba ka ‘yar sa ka aura. A ƙarshe, ko ka ƙi ko ka so ka zama Bahaushe. Wannan halayya ta haɓaka zamantakewa da cinikayya da maƙwabta na kusa da na nesa ita ce abin da ya haɓaka cibiyoyin kasuwanci da Ilimi irin su Kano da Katsina.
Duk da cewa Jihadin Fulani ƙarƙashin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya karɓe ikon mulki daga hannun Hausawa, amma halayyar Bahaushe ta karɓar baƙi ta sa sun cinye Fulani a jihadin zamantakewa, yadda Fulani suka narke suka zama Hausawa ƙarfi da yaji.
Zaluncin masarautu kan talakawa (walau asalin Hausawa ko Fulani) da zuwan Turawa wanda ya daɗa ƙarfafa sarakuna, da kawo siyasar dimokiraɗiyya ya janyo zaizayewar duk wasu halaye na kirki da aka san Hausawa da su. Tun daga samun mulkin kai, shugabanni na farar hula da soja sun ci gaba da assasa ƙabilanci, ɓangaranci na addini da dawo da bautar shugabanni a faɗin Arewa da Nijeriya. An wayi gari wasu ƙalilan sun dafe madafan Iko yadda daga su sai ‘ya’yan su.
A yau an wayi gari babu wanda ya fi Bahaushe yawan ‘ya’ya da ke almajiranci. Almajiranci ya zama al’ada mafi muni a zamantakewar Bahaushe yadda aka jingina ta da addini na ƙarya. Domin a baya kowa ya san yadda ake almajiranci, abin da ya faro daga fadar Annabi, sannan aka inganta shi ƙarƙashin daular Andalusiya, abin da ya bai wa Turawa damar kwaikwayon sa yadda ya haifar da jami’o’i na zamani. Amma da Bature ya zo Arewa sai ya kassara wannan tsari na asali wanda shi ne rumbu da al’ummar Hausawa ke zaƙulo malamai, limamai da alƙalai. A ƙarshe sai aka juyar da almajiranci ya zama bara.
Akasarin Fulani, tun daga Jihadin Ɗanfodiyo, sun narke sun zama Hausawa a cikin birane. Duk wata al’ada ta Fulatanci, kama daga yare, al’ada da tsarin zamantakewa, duk sun ɓace a cikin birane. Fulani makiyaya kuma suna daji yadda ba su da wani tsari face bautar shanun su, ‘ya’yan su na cikin duhun jahilci. Fulani iri na mun zama Hausawa ko muna so ko ba ma so, ballantana ba mu da wani abin alfahari da ya wuce na Hausa.
Ni abin da na karanta a jami’a shi ne Hausa da Ilimin Islama. Ba ni da wani yare da al’ada da ya wuce Hausa. To, yanzu kawai sai wani ya ce dole sai na zaɓi ɓangaren Hausa zalla ko Miyetti Allah? Kamar akwai jahilci cikin wannan buƙata, ko?
Idan zuciyar ka da dattin ƙabilanci a cikin ta, shi kaɗai kake iya gani. Idan wani ya ce ga ruwa wanke dattin sai ka ɗauka wuta ya miƙa maka. Kamar yadda Allah ya bayyana kafirai da summum bukumum umyun. Don haka ni ban taɓa harin canza tunanin mai mafarkin cewa akwai wani abu wai shi Hausa Zalla ba da manufar raba kan mu, saboda shi zallar jahilci ba shi da magani!
Ina kira ne kawai ga masu hankali da imani su fahimci ƙabilancin Bafulatani ko Bahaushe ko Bayarabe ba shi da hurumi a Musulunci, haram ne. Kai da ka halatta shi kada Allah ya sa ka daina.
Ka kuma duba baya daga san da kuka fito da wannan da’awa ta zaluncin da kuke wa kan ku, wace riba ƙwaya ɗaya ta haifar wa mutanen da kuke kira da Hausawan? Ko kuma akwai wata mafita guda da aka kawo na tarin matsaloli da ke addabar Hausawan?
Kira na ga matasa shi ne su gane cewa babu wata annoba da ake ƙoƙarin kunno musu a yau wadda ta wuce wannan maganar ta Hausa Zalla a Arewa. Haƙiƙa, kafa ƙungiya don kare muradu ko yaɗa manufofin kirki na wasu mutane ba laifi ba ne, ‘yanci ne na kowa da kowa. Amma kafa ƙungiya, da manufar assasa ƙabilanci da rarrabuwar kai da gina gaba, kamar yadda ‘yan Hausa Zalla ke ƙoƙarin yi, haramun ce.
Gwari-gwarin da’awa ta shi ne: na farko ba na buƙatar duk wani mai iƙirarin Hausa Zalla ya yarda da ni ko ya fasa da’awar sa ta mugun nufi. Don haka kada ka ɓata lokacin ka domin ganin sai lallai mai da’awar mugun nufi ya janye ta. Su ci gaba, ko ma in ce, “Allah ya tsine wanda ya fasa!”
Buƙata ta ita ce mutane masu hankali da imani da adalci su fahimci haɗarin ƙabilanci, ba na Hausa Zalla kaɗai ba, har ma da na Fulani da Barebari da Yarabawa da Larabawa, Turawa da ma kowane irin ƙabilanci abin banza ne da a tarihi babu abin da ya haifar sai fitina da koma-baya.
Na san dai yau a duniya babu ƙabila mafi koma-baya, jahilci, talauci da rashin tsaro irin mu. To idan ba mu da lokacin haɗuwa a matsayin al’umma mai yare, al’adu da addini guda domin tunkarar waɗannan abubuwa, amma muna da lokacin ƙara kunno wa kan mu wutar gaba da juna… to haƙiƙa sai in ce lallai tsinuwar Allah ta tabbata a kan mu.
Amma dai ita bari ba shegiya ba ce. Kowa ya ɗora a tafarkin da ya zaɓa.
* Malam Ali Abubakar Sadiq, marubuci mai sharhi kan al’amurran yau da kullum, mazaunin Kano ne






