• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Cikar wa’adin ƙarfafa jari: Yadda bankunan Nijeriya suka bazama tara Naira tiriliyan 4.6 a ƙoƙarin cika sharuɗɗan CBN

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
March 30, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Cikar wa’adin ƙarfafa jari: Yadda bankunan Nijeriya suka bazama tara Naira tiriliyan 4.6 a ƙoƙarin cika sharuɗɗan CBN
Bankunan Nijeriya

Bankunan Nijeriya

Bankunan kasuwanci a Nijeriya sun shiga wani sabon mataki na gasa mai zafi, yayin da bankuna 33 da suka samu nasarar tara kusan naira tiriliyan 4.6 a ƙarƙashin shirin ƙarfafawa da bunƙasa jari na Babban Bankin Nijeriya (CBN), wanda wa’adin sa ke cika a ranar Talata, 31 ga Maris 2026.

Wannan ya haifar da abin da masana ke kira gasa tsakanin sassa don samun damar bayar da rance mai cike da samun tagomashi.

Bincike ya nuna cewa tara wannan jari, wanda aka samu ta hanyoyi daban-daban kamar haƙƙin sayen hannun jari (rights issue), sayar da hannun jari ga jama’a, saka hannun jari daga masu zaman kan su, da kuma haɗin gwiwa, ya ba bankunan damar cika wa’adin da hukuma ta gindaya, tare da ƙarfafa ƙididdigar adadin kuɗaɗen su da kuma ikon ɗaukar manyan ayyukan ba da rance.

Wa’adin Naira Biliyan 500 Mafi Ƙarancin Jari:

Bankunan ƙasa da ƙasa na ne aka ba wannan umarni da wa’adi, a ƙarƙashin sabon tsarin ƙarfafa jarin CBN ya gindaya. Bankunan kasuwanci masu lasisin aiki a ƙasashen waje dole ne su mallaki aƙalla naira biliyan 500 a matsayin jarin da aka biya, wanda ya ninka sau tara daga tsohon adadi na naira biliyan 50.

Duk da shakku da aka fara yi kan ko kasuwa za ta iya ɗaukar wannan nauyin, “Manyan Bankuna Bakwai” ba wai sun cika sharadin kawai ba ne, har ma wasu sun zarce adadin.

Access Holdings Plc, waso Access Bank ya zama na farko da ya kammala wannan aiki, inda ya tara naira biliyan 351.01 ta hanyar amfani da tsarin dijital na NGX. Wannan ya ɗaga jarin bankin zuwa naira biliyan 600, wanda ya zarce adadin da aka nema.

Zenith Bank Plc shi ma ya nuna ƙarfin sa, inda ya tara naira biliyan 289.44 ta hanyoyin haɗaka. Babbar Daraktar Access Bank, Dakta Adaora Umeoji, ta bayyana cewa an yi wannan ne domin haɓaka girma da kuma faɗaɗa aiki zuwa yankunan ƙasashe rainon Faransa a Afrika ta hanyar reshen Paris. Jimillar jarin bankin yanzu ya kai naira biliyan 614.65.

Guaranty Trust Holding Company (GTCO) ya ƙara jarin GTBank zuwa naira biliyan 504 bayan tara naira biliyan 365.85. Haka kuma ya zama bankin farko a Afrika ta Yamma da ya yi rajista a kasuwannin hannun jari biyu—NGX da London Stock Exchange—inda ya samu dala miliyan 105 daga masu saka jari na ƙasa da ƙasa.

Fidelity Bank ma ya yi fice, inda ya tara naira biliyan 272.95, tare da yawan masu neman sayen hannun jarin da ya zarce kima sosai.

Sauran bankuna kamar UBA, FCMB, da First Bank su ma sun tabbatar da matsayin su, inda First Bank ke shirin kai jarin sa zuwa naira biliyan 748.

Ƙarfafuwar Bankunan Kasa da na Yanki:

A ɓangaren bankunan ƙasa da na yanki, labarin ya ta’allaka ne kan haɗewa da kuma tallafin kamfanoni.

Bankunan ƙasa, waɗanda ake buƙatar su jarin kowanen su ya kai naira biliyan 200, sun nuna ƙwazo sosai.

Stanbic IBTC Holdings ta cimma wannan buri bayan tara naira biliyan 181.4, tare da ƙarin masu sayen hannayen jari da ya kai kashi 21.9%.

Ga bankunan waje kamar Ecobank Nigeria, Standard Chartered da Citibank, sun samu damar cika sharadin ne ta hanyar tallafin kamfanonin su na waje. Misali, Ecobank ya samu dala miliyan 125 daga uwar kamfanin sukutum.

Babban abin lura a wannan rukuni shi ne haɗewar Providus Bank da Unity Bank, inda CBN ya bada tallafin naira biliyan 700 domin tabbatar da ɗorewar sabon bankin.

A gefe guda, Wema Bank ya kai sama da naira biliyan 200 bayan tara naira biliyan 150 ta hanyar wasu hanyoyi daban-daban.

A rukunin bankunan yanki da na kasuwanci (merchant banks), inda ake buƙatar naira biliyan 50, bankuna kamar Nova Bank, Parallex Bank da Titan Bank sun cika sharadin. Haka kuma bankunan kasuwanci irin su Rand Merchant Bank, Coronation da FSDH sun daidaita jarin su.

Bangaren bankunan da ba sa karɓar kuɗin ruwa, an samu gagarumin cigaba.

Jaiz Bank, wanda shi ne ya fara irin wannan tsarin a Nijeriya, yana kan gaba da jarin naira biliyan 47.9—fiye da sau biyu na abin da ake buƙata, wato naira biliyan 20.

Wannan ya samu ne bayan tara naira biliyan 10.04.

Sauran bankuna kamar Lotus Bank, Taj Bank, da The Alternative Bank duk sun cika sharadin, yayin da Summit Bank ya shiga a matsayin bankin yanki da jarin naira biliyan 15.3.

Tags: bankunaCBNjariOlayemiCardoso
Previous Post

Hausa Zalla Ko Zallar Jahilci?

Next Post

Gwamnatin Tarayya na shirin tallafa wa gidaje miliyan 15 ta hanyar HoPE-CT – Ministan Yaɗa Labarai

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Ba da yawu na Sa’idu Enagi ya yi rubutu kan siyasar Neja ba, kuma na dakatar da shi – Ministan Yaɗa Labarai

Gwamnatin Tarayya na shirin tallafa wa gidaje miliyan 15 ta hanyar HoPE-CT – Ministan Yaɗa Labarai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!