Ma’aikatan jirgi huɗu sun mutu bayan wani jirgin ɗaukar mai na Sojin Sama na Amurka ya faɗi a Iraƙi ranar Alhamis, kamar yadda Babbar Rundunar Yaƙi ta Amurka (US Central Command) ta bayyana a safiyar Juma’a.
Jaridar New York Post ta ruwaito a gidan yanar ta yau Asabar cewa jirgin man na Amurka mai suna KC-135 Stratotanker yana ɗauke da ma’aikata shida a cikin sa lokacin da aka rasa shi a sararin samaniya na yankin da ake da alaƙar abota da su, a wani lamari da ya faru a daidai lokacin yaƙin da Amurka da Isra’ila suke kai wa Iran mai taken “Operation Epic Fury.”
“Har yanzu ana binciken yadda lamarin ya faru. Sai dai rasa jirgin bai faru sakamakon harbin abokan gaba ko kuma harbin kuskure daga abokan hulɗa ba,” inji sanarwar.
Jirage biyu ne dai suka shiga cikin lamarin, inda jirgi na biyu ya sauka lafiya.
Sojojin Amurka sun ce za su ɓoye sunayen ma’aikatan sojin da suka mutu har sai bayan awanni 24 bayan an sanar da iyalansu.
Sai dai kuma ƙungiyar gwagwarmayar mai suna Islamic Resistance in Iraq, wadda gangamin ƙungiyoyin mayaƙa ce masu samun goyon bayan Iran, ta ce ita ce ta harbo jirgin a yammacin ranar Alhamis.
A cikin wata sanarwa, ƙungiyar ta ce ta kakkaɓo jirgin ɗaukar mai ɗin na sojin ne “don kare ikon ƙasar mu da sararin samaniyar ta.”
Shi dai irin wannan jirgi, yakan ba jirgin sama mama ne (wato mai) a sararin samaniya ba tare da sun sauko ƙasa ba.







