Ɗan Majalisar Wakilan Amurka, Riley M. Moore, ya zargi ‘yan ƙasar Chana da ke haƙar ma’adinan ƙarƙashin ƙasa ba bisa ƙa’ida ba a Nijeriya da tallafa wa ta’addanci a ƙasar.
A wani saƙo da ya wallafa a dandalin X, Moore ya yi iƙirarin cewa masu gudanar da ayyukan haƙar ma’adinan daga Chana suna tafiyar da harkokin su ba bisa doka ba, tare da biyan abin da ya kira “kuɗin kariya” ga ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayin addinin Musulunci.
Ya zargi cewa ana amfani da waɗannan kuɗaɗe wajen ɗaukar nauyin ayyukan tashin hankali, ciki har da hare-haren da ake kai wa Kiristoci.
Moore ya ce ya miƙa rahoto ga Shugaban Amurka, Donald Trump, a farkon makon nan, inda ya bayyana abin da ya kira musgunawa da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya.
Har zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Chana ko kuma hukumomin Nijeriya dangane da waɗannan zarge-zarge. (DW)







