• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Minista ya taya gidan rediyon Zuma FM Suleja murnar cika shekara 20 tare da haɓaka labaran aikin gona

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
December 13, 2025
in Labarai
A A
0
Minista ya taya gidan rediyon Zuma FM Suleja murnar cika shekara 20 tare da haɓaka labaran aikin gona
Ma'aikata a bakin aiki cikin situdiyon gidan rediyon Zuma FM a Suleja

Ma'aikata a bakin aiki cikin situdiyon gidan rediyon Zuma FM a Suleja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya taya gidan rediyon Zuma 88.5 FM da ke Suleja a Jihar Neja murnar cika shekara 20 da kafuwa, tare da zagayowar karo na 9 na Bikin Girbin Noma na Zuma.

Tashar Zuma FM Suleja takan mai da hankali ne wajen ba da labaran aikin gona, kuma takan shirya bikin baje-kolin kayayyakin aikin gona a duk shekara.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a yau Asabar, Idris ya ce wannan cika shekara ta 20 wani muhimmin mataki ne wanda “ba wai murnar doguwar ɗorewar ku kawai ba ce, har ma shaida ce ta ƙarfin hangen nesan ki, daidaito, da hidimar al’umma.”

Ya ƙara da cewa: “A matsayin ta na tashar rediyo mai zaman kan sa ta farko a Jihar Neja, Zuma FM ta taka rawar gani a tarihi wajen faɗaɗa samun bayanai, ƙarfafa muryoyin al’ummomin karkara, da haɓaka sadarwar noma ta hanyoyin da ke ci gaba da inganta rayuwar al’umma a Arewa.

“Ƙudirin ku na tasirin zamantakewa da bunƙasa karkara yana wakiltar ainihin ma’anar watsa shirye-shirye mai ɗa’a.”

Ministan ya yaba wa shugabanni, ma’aikata da abokan hulɗar gidan rediyon waɗanda suka ɗore da wannan aiki nasu tsawon shekaru ashirin, yana mai cewa: “Ayyukan ku sun yi daidai da ƙoƙarin mu na ƙasa wajen gina Nijeriya mai wayewa, haɗin kai, da cigaba.

“Ina taya ku murna karo na biyu bisa wannan muhimmin biki. Ina sa ran kasancewa tare da ku a wannan tarihi mai muhimmanci.”

Tags: Mohammed Idristaya murnaZuma FM Suleja
Previous Post

Tsare-tsaren harkar kiwon lafiya na Tinubu suna magance gudun hijirar ƙwararru da ƙarfafa aikin likita – Ministan Yaɗa Labarai

Next Post

Gasar Firimiya: Palmer ya zura ƙwallo yayin da Chelsea ta dawo hanyar nasara a kan Everton

Related Posts

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500
Labarai

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

May 13, 2026
Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Next Post
Gasar Firimiya: Palmer ya zura ƙwallo yayin da Chelsea ta dawo hanyar nasara a kan Everton

Gasar Firimiya: Palmer ya zura ƙwallo yayin da Chelsea ta dawo hanyar nasara a kan Everton

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!