Ƙoƙarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake yi haiƙan suna ci gaba da magance matsalar gudun hijirar ƙwararru tare da ƙarfafa bunƙasar harkar likitanci a Nijeriya, inji Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris.
Ya bayyana hakan ne a bikin rantsarwa karo na huɗu (Fourth Attestation Ceremony) na ɗaliban ajin koyon aikin likita na shekarar 2025 a Jami’ar Nile ta Nijeriya, wanda aka gudanar a ranar Juma’a a Abuja.
Ya ce: “Mun ga abin da Shugaban ƙasa ya yi; ya ƙaddamar da cibiyoyin kula da cutar daji guda shida a faɗin ƙasar nan, sannan kuma ya fara gyaran dukkan manyan cibiyoyin kiwon lafiya.”
Idris ya ƙara da cewa, “Wannan alama ce wadda ke nuna cewa tsarin kiwon lafiya na Nijeriya yana kan hanyar sa ta zama irin na manyan ƙasashen duniya, sakamakon manufofi masu ƙarfafawa da ke haɓaka masana’antar likitanci.”


Ministan ya ce ya dace ƙwararrun likitoci da sauran ma’aikatan lafiya su daidaita kan su da hangen nesa na Shugaba Tinubu, wanda ke aiki tuƙuru don tabbatar da cewa duk ƙwararru suna da damar aiki cikin kwanciyar hankali a cikin Nijeriya, maimakon barin ƙasar da wasun su ke yi.
Ya ƙara da cewa ɓangaren kiwon lafiya yana ci gaba da inganta a kullum, ta hanyar farfaɗo da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (primary healthcare facilities), da kuma zuba jari da kuɗaɗe, wanda ke ƙara haɓaka harkar likitanci a ƙasar nan.
Daga cikin ɗalibai 58 da suka halarci bikin rantsarwar, bayan sun kammala karatun Digirin Likitanci da Tiyata (MBBS) a Jami’ar Nile ta Abuja bayan shekaru shida na tsananin karatu, akwai ‘yar Ministan, wato Ruƙayya Mohammed Idris, wadda ta yi rantsuwar aiki da alƙawarin bin ƙa’idojin aikin likitanci, abin da ya ƙayatar da iyayen su da masu kula da su.








