A yau ne tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya karɓi baƙuncin Mataimakin Shugaban Jami’ar Jos, Jihar Filato, Farfesa Tanko Ishaya, da ‘yan rakiyar sa.
Sun ziyarce shi ne domin neman agajin sa wajen shirya Gasar Ƙungiyoyin Wasanni ta Jami’o’in Nijeriya, wato Nigerian University Games Association (NUGA), kashi na 27, wanda zai a jami’ar kwanan nan.
Sun faɗa masa muhimmancin ɗaukar nauyin bikin gasannin, musamman yanzu da ake ƙoƙarin shawo kan rikice-rikicen ƙabilanci da addini da akan yi a Filato, da taimaka wa matasa.

Atiku ya ce ya fahimce su sarai, musamman da yake shi ma yana da tasa jami’ar, wato American University of Nigeria (AUN).
Ya ce ya yi murna da suka ga dacewar sa har suka kai masa wannan tayin tare da naɗa shi ɗaya daga cikin Iyayen gasar “Jos 2025 NUGA” kuma ya yi masu alƙawarin zai taimaka ɗin.







