• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata masu cewa ana yi wa Kiristocin Nijeriya kisan ƙare dangi 

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
September 28, 2025
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata masu cewa ana yi wa Kiristocin Nijeriya kisan ƙare dangi 
Alhaji Mohammed Idris

Alhaji Mohammed Idris

 

Gwamnatin Tarayya ta yi Allah-wadai tare da ƙaryata zarge-zargen da wasu kafafen watsa labarai na ƙasashen waje da masu tasiri a kafafen sada zumunta suke yi na cewa wai ‘yan ta’adda a Nijeriya suna yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Gwamnatin ta ce irin wannan iƙirarin “ƙarya ne, marasa tushe, abin ƙyama, kuma na raba kawuna.”

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce: “Bayyana matsalolin tsaro a Nijeriya a matsayin wani yaƙi da aka kitsa musamman kan wasu mabiya addini guda ɗaya ba daidai ba ne, kuma rashin adalci ne.”

Ya ƙara da cewa: “Ko da yake Nijeriya, kamar dai wasu ƙasashen, tana fuskantar matsalolin tsaro, ciki har da ta’addanci da ‘yan ta’adda suke aikatawa, fassara wannan a matsayin wani hari na musamman kan Kiristoci ba gaskiya ba ne, illa ma cutarwa ne.

“Hakan na wofintar da matsala mai matuƙar rikitarwa, kuma yana taimaka wa ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifi wajen raba kan ‘yan Nijeriya bisa addini ko ƙabila.”

Idris ya ce: “Ayyukan ta’addanci ba su taƙaita ga wata al’umma ta addini ko ƙabila ɗaya ba. Waɗannan miyagun suna kai hari ga duk wanda ya ƙi bin aƙidar su ta kisa, ko Musulmi, ko Kirista, har ma wanda ba ya bin wani addini. Duk suna shan wahala a hannun su.”

Ya nuna cewa Gwamnatin Tarayya tana da cikakken ƙudirin murƙushe ƙungiyoyin ta’addanci da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa, kuma wannan tuni aka riga aka fara ganin sakamakon sa.

Ya ce: “Tsakanin watan Mayu na 2023 da Fabrairun 2025 kaɗai, an hallaka ‘yan ta’adda da masu laifi sama da 13,543 tare da kuɓutar da kusan mutum 10,000 daga hannun su a faɗin ƙasar nan. A watan da ya gabata ma, an cafke manyan shugabannin ƙungiyar ANSARU, ƙungiyar da ke da alaƙa da Al-Ƙa’ida, a wani babban samamen yaƙi da ta’addanci. Sun haɗa da Mahmud Muhammad Usman (wanda aka fi sani da Abu Bara’a/Abbas/Mukhtar), wanda ke kira kan sa Sarkin ANSARU, da kuma Mahmud al-Nijeri (wanda aka fi sani da Malam Mamuda), wanda ya kasance mataimakin sa.”

Ministan ya ce waɗannan nasarorin wata hujja ce ta jajircewar jami’an tsaro da kuma rashin ingancin zargin cewa Nijeriya tana lamunta da ta’addancin da ya ta’allaƙa da addini.

Ya ƙara da cewa: “Gwamnatin Tarayya ba ta yi ƙasa a gwiwa ba a aikin ta na kare kowane ɗan Nijeriya, ba tare da la’akari da addini ko ƙabilar sa ba. Rundunar Sojojin Nijeriya da ta ‘Yan Sandan Nijeriya kuma suna gudanar da kotunan soja da shari’o’i don hukunta jami’an da suka karya doka. Wannan na nuni da muhimmancin ladabi da bin doka a hukumomin tsaro.”

Ya jaddada cewa Nijeriya ƙasa ce mai addinai da dama, wadda ke ɗauke da manyan al’ummomin Musulmi da Kiristoci a duniya. “Kiristanci ba ya cikin haɗari ko kuma ana nuna masa wariya a Nijeriya,” in ji shi.

Ya kuma yi nuni da cewa: “Shin waɗannan masu saka baki daga ƙasashen waje sun san cewa manyan hafsoshin Rundunar Sojojin Nijeriya da ‘Yan Sandan Nijeriya a yanzu dukkansu Kiristoci ne? Wannan kansa na nuna yadda jagorancinmu ya kasance na haɗin kai.”

Game da yaƙi da ta’addanci, Ministan ya bayyana cewa an yi nasarar gurfanar da wasu ‘yan Boko Haram a gaban kuliya: “Zuwa yanzu, an yi nasarar gurfanar da rukuni bakwai na waɗanda ake zargi, inda aka samu hukunci sama da 700. A yanzu muna shiga zagayen takwas na shari’ar, don nuna tsananin ƙudirin mu wajen yaƙar ta’addanci da masu ɗaukar nauyinsa.”

A cewars sa, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, gwamnati za ta ci gaba da ƙoƙari don tabbatar da adalci da ƙara tsaro.

“Labarin Nijeriya ba na kisan ƙare dangi na addini ba ne. Labarin ƙasa ce mai juriya, bambance-bambance, da ƙudiri na haɗin kai wanda duniya ta shaida.”

Ya tuna cewa a watan Maris na bana, lambar yabo ta farko ta Commonwealth Peace Prize an bai wa shugabannin addinai biyu na Nijeriya — Fasto James Movel Wuye da Liman Muhammad Nurayn Ashafa — saboda aikin su na gina amana da haɗin kai tsakanin Musulmi da Kiristoci.

Ya ce: “Wannan na nufin cewa Nijeriya ba wai kawai tana fitar da al’adu da kiɗa zuwa duniya ba ne, har ma tana fitar da tabbataccen tsari na musamman na zaman lafiya tsakanin addinai.”

A ƙarshe ya yi kira ga kafafen watsa labarai na duniya da masu sharhi su guji rashin sani da yin tashe-tashen hankula ta hanyar kalaman rarraba kawuna. “Maimakon haka, ya kamata a tallafa wa ƙoƙarin Nijeriya na ci gaba da yaƙar ta’addanci da duk wani irin laifuka,” inji shi.

Previous Post

Masu wulaƙanta naira ke ƙara haifar da tsadar buga sababbin kuɗi – CBN

Next Post

Tsakanin Ɗangote da PENGASSAN

Related Posts

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500
Labarai

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

May 13, 2026
Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Next Post
Tsakanin Ɗangote da PENGASSAN

Tsakanin Ɗangote da PENGASSAN

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!