Irin tankiyar da ake tsakanin Ɗangote da PENGASSAN za a riƙa samun ta a wannan lokacin da manyan abubuwa suke ƙaura daga hannun gwamnati zuwa hannun ‘yan kasuwa.
A aikin gwamnati akwai kariya da ma’aikaci ke samu na cigaban aikin sa muddin ba laifi ya aikata ko matsala ta shafi ma’aikatar sa ba. Illar wannan a Nijeriya shi ne ya haifar da wofantar da aiki da ma’aikata da yawa suke yi kuma ofishin Shugaban Ma’aikata da ƙungiyoyin ƙwadago suna hana ladabtar da su kamar yadda doka ta tanada.
Wannan rashin ladabtarwa shi ne babban dalilin lalacewar aikin gwamnati da hukumomin ta da kamfanonin ta waɗanda aka kafa don amfanin jama’a.
Da aka lalata na gwamnati sai aka samu giɓi da ‘yan kasuwa suka shigo suka kafa nasu kamfanonin akasari da kuɗaɗen jari da ya haɗa da na ‘yan ƙasashen waje. A nan, dole abin ya taho da matsaloli biyu amma idan aka sa hankali a lamarin za a iya warware su.
Matsalar Ma’aikaci
Na farko, dole ma’aikata su sani cewa ba za su samu kariya irin wadda suke da ita a gwamnati ba. Kasuwanci ba ya aiki da haka. Dole su tashi tsaye su yi ta aiki wurjanjan ko da a albashi da bai kai na gwamnati ba a sau da yawa. In kuwa ba su yi, su ajiye aikin su tafi su nemi wani wajen kamar yadda da yawa suka yi hatta a Matatar Ɗangoten.
Haka ita ma gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago ba za su iya bai wa ma’aikaci kariya a kamfanin ɗan kasuwa ba a ko wane hali kamar yadda suka saba yi a na gwamnati. Amma suna iya shiga tsakani a kan abin da bai shafi laifi ba ko haƙƙin ɗan kasuwa ba wanda doka ta ba shi.
Matsalar Ɗan Kasuwa
Matsala ta biyu ita ce ta ɗan kasuwa. Burin sa riba ne, ba kyautata wa al’umma ba. Haka Adam Smith ya ce. A wajen neman riba, in aka bar shi, zai iya aikata komai, kuma ya take kowa. A nan dole a taka masa birki.
Masu taka masa birki Allah ne da dokokin ƙasa. Dole ya ji tsoron Allah, musamman in ya yi imanin haɗuwa da Shi, kar ya ci zalin ma’aikatan sa, amma ya ba su haƙƙin su bisa adalci har ma ya kyautata masu saboda Allah na son masu kyautatawa. In ya ƙi, ya yi gaban kan sa, to Allah na madakata yana jiran sa.
Dole kuma gwamnati da kotuna su tabbatar sun samar da dokoki da za su hana cin zalin ma’aikata da musguna masu. Waɗannan dokoki idan akwai su dole a tashi tsaye wajen dabbaka su. Haƙƙin ‘yan ƙasa ne da ya zama wajibi a kan ɓangarorin gwamnati guda uku duka. Inda dokokin suka gaza, sai majalisa ta kyautata su amma ba tare da sun ɗaure hannun ‘yan kasuwa ba ta yadda za a koma gidan jiya inda ma’aikata da ƙungiyoyin su za su lalata kasuwancin kamar yadda suka lalata na gwamnati a baya.
Kira
A ƙarshe, babban kira na a nan shi ne sassan biyu su wa Allah su sasanta tsakanin su. Kai Ɗangote ka yi abin da Allah ya ce. Ka duba ƙorafin ma’aikatan ka ‘yan Nijeriya ka ba su daraja kamar yadda kake bai wa Indiyawan da ka kawo. An sani akwai kuɗaɗen da za ka kashe wa ‘yan ƙasar waje waɗanda a ƙa’ida ba sai ka kashe wa ‘yan Nijeriya ba saboda bambancin rayuwa tsakanin ƙasashen su da nan. Ma’aikatu na waje da yawa haka suke yi. Amma, aƙalla, mafi ƙarancin albashin su ya kasance ɗaya ko kar tazarar ta yi yawa. Kuma, aƙalla, ka biya su kusan abin da sauran ‘yan kasuwa—kamar BUA, Shell, Otedola da sauran su—suke biyan nasu ma’aikatan. Kar giyar kaka-gida (monopoly) ta kwashe ka ka ce abin da ka ga dama za ka yi don ba yadda Nijeriya ta iya da kai a harkar mai a yanzu, kai ne kaɗai damisa a fage. La! La!
Ku kuma PENGASSAN, dole ku sani zamani ya wuce da za ku ci karen ku ba babbaka a Nijeriya. Idan kuna tuhumar Ɗangote da karya dokar ƙwadago, ba rufe matatar sa da tirsasa shi da ƙarfi zai gyara abin ba. Kotu ce ke da haƙƙin tirsasa shi idan ta tabbatar da laifin sa. Don haka sai ku maka shi a kotu. To a nan ne za a warware matsalar lokaci guda har a bada hukunci da zai yi amfani nan gaba idan yanayi irin wannan ya taso. In ba haka ba, mu ‘yan Nijeriya ku za mu ɗora wa laifi.
Fata
Ina fata Allah ya sa ɓangarorin biyun su daidaita tsakanin su. Mu dai fatar mu a samar da sauƙin rayuwa a Nijeriya ta hanyar bunƙasa tattalin arziki da zamantakewa tagari, da fahimtar juna da bin doka.
Allah ya taimake mu.
* Dakta Aliyu Usman Tilde mai sharhi ne kan al’amurran yau da kullum






