• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Cewar Sarkin Zazzau: An yi wa rawar da El-Rufai ya taka wajen naɗa ni sarauta gurguwar fahimta

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
September 13, 2026
in Labarai
A A
0
Cewar Sarkin Zazzau: An yi wa rawar da El-Rufai ya taka wajen naɗa ni sarauta gurguwar fahimta
Gwamnan Jihar Kaduna na lokacin, Malam Nasir El-Rufai, yana miƙa wa sabon Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, sandar sarauta

Gwamnan Jihar Kaduna na lokacin, Malam Nasir El-Rufai, yana miƙa wa sabon Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, sandar sarauta

Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, ya ce an yi wa rawar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya taka wajen zamowar sa Sarkin Zazzau mummunar fahimta.

Ya ce alaƙar da ke tsakanin su ta samo asali ne musamman daga dangantakar iyali.

Bamalli, wanda a watan Oktoba zai cika shekaru shida a kan karagar mulki, ya bayyana cewa El-Rufai ɗan’uwan mahaifin sa ne, yana mai jaddada cewa bai kamata a fassara alaƙar tsohon gwamnan da shi da cewa ita ce ta haifar da naɗa shi sarki ba.

Ya ce: “Ni kawun sa ne. Ni ɗan’uwan mahaifin sa ne. Ni da Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, mu ne kawunnan shi. Wannan ce alaƙar da ke tsakanin mu.”

Sarkin ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar Weekend Trust, gabanin cikar shekaru shida da hawan sa karagar mulki.

Bamalli ya ce sau da yawa ana fahimtar yanayin da ya kai ga naɗa shi sarauta ba daidai ba, musamman saboda a lokacin da marigayi Sarkin Zazzau, Shehu Idris, ya rasu a watan Satumba 2020, shi yana ƙasar waje.

A lokacin, yana aiki a matsayin Jakaden Nijeriya a Thailand, tare da wakilcin Nijeriya a Myanmar, kuma dole ne ya yi shirye-shiryen dawowa gida a lokacin da aka saka dokar kulle sakamakon annobar korona.

A cewar sa, sai da ya biya dala 9,000 domin dawowa Nijeriya tare da matar sa da ’ya’yan sa mata biyu, saɓanin iƙirarin cewa El-Rufai ne ya yi hayar jirgin sama domin dawo da shi gida.

“Ni ne na biya; rasiɗan suna nan. Ko kuma ku bincika Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Bangkok. Su ne suka biya kuɗin dawowa ta gida ni da iyali na. Mun biya dala 9,000 kuma muka dawo gida,” in ji shi.

Bamalli ya ce rawar da El-Rufai ya taka ta bayyana ne bayan ya iso filin jirgin sama na Abuja, inda wani mataimakin gwamnan mai suna Peter ya gan shi tare da sanar da tsohon gwamnan cewa ya iso.

Ya ce daga nan El-Rufai ya ba da umurnin cewa motocin sa su kai Zariya shi da iyalin sa, bayan mutumin da aka tura ɗauko shi daga filin jirgin ya rasa jirgin sa.

Sai dai Sarkin ya ce tun kafin hakan ya riga ya yi shirin tafiya Kaduna ta jirgin ƙasa, kafin daga bisani ya amince da tayin da aka yi masa.

Sarkin ya kuma bayyana cewa tun farko bai yi niyyar shiga takarar neman sarautar ba, sai dai daga bisani aka matsa masa ya shiga tseren neman gadon sarautar.

Tags: Ahmed Nuhu BamalliMalam Nasir El-RufaisarkiZazzau
Previous Post

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

Next Post

Taƙaitaccen Tarihin Ɗanwaire Da Ƙasar Ruma

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post

Taƙaitaccen Tarihin Ɗanwaire Da Ƙasar Ruma

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!