Tawagar ‘yan jarida da ke gudanar da rangadin ‘Gani Ya Kori Ji’ na manyan ayyukan Gwamnatin Tarayya a Arewacin Nijeriya ta kai ziyara aikin sake gina babbar hanyar Abuja–Kaduna, inda ta gano cewa aikin ya kai kusan kashi 85 cikin ɗari na kammaluwa.
Tawagar, wadda Babban Mai Taimaka wa Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Malam Abdulaziz Abdulaziz, ke jagoranta, ta ziyarci aikin ne bayan kammala duba aikin Kaduna Western Bypass da kuma tashar Green Ville CNG da ke jihar Kaduna.
A yayin ziyarar, jami’an da ke kula da aikin sun yi wa tawagar bayani kan yadda aikin ke gudana, inda suka ce an kammala kusan kashi 85 cikin ɗari na sake gina titin. Sun kuma bayyana cewa ana ci gaba da aikin cikin inganci da sauri domin kammala shi cikin wa’adin da aka tsara.
Sun bayyana cewa titin Abuja–Kaduna yana daga cikin muhimman hanyoyin da ke haɗa Babban Birnin Tarayya da jihohin Arewa, yana taka muhimmiyar rawa wajen zirga-zirgar matafiya, jigilar kayayyaki da bunƙasa harkokin kasuwanci.
A cewar su, idan aka kammala aikin gaba ɗaya, zai rage lokacin tafiya, sauƙaƙa cunkoson ababen hawa, inganta tsaron masu amfani da hanya tare da ƙara bunƙasa tattalin arzikin yankunan da titin ya ratsa.
Jami’an aikin sun kuma bayyana cewa ana sake gina titin ne da kankare mai ƙarfi (reinforced concrete pavement) maimakon kwalta, domin tabbatar da ɗorewar titin, rage yawan lalacewar sa da kuma tsawaita rayuwar sa.
Sun ce aikin yana daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu take aiwatarwa a ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda), da nufin inganta ababen more rayuwa da ƙarfafa haɗin kai tsakanin sassan ƙasar nan.
Da yake jawabi bayan rangadin, Malam Abdulaziz Abdulaziz ya bayyana hanyar Abuja–Kaduna a matsayin ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin sufuri a Nijeriya, yana mai cewa Gwamnatin Tarayya ta ba aikin fifiko saboda muhimmancin sa ga tattalin arziki da haɗa yankunan ƙasar.
Ya ce shirin ‘Gani Ya Kori Ji’ na bai wa masu aikin jarida damar ganin cigaban manyan ayyukan gwamnati da idon su, domin su isar wa al’umma sahihan bayanai kan irin cigaban da ake samu.
Tawagar ta yaba wa Gwamnatin Tarayya da Ma’aikatar Ayyuka bisa yadda aikin yake tafiya, tare da bayyana fatan cewa kammala titin zai ƙara sauƙaƙa zirga-zirga, inganta tsaro da kuma amfani ga miliyoyin ‘yan Nijeriya masu amfani da hanyar Abuja–Kaduna.







