
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kaduna ta kama wasu mutum shida da ake zargi da hannu a kisan wasu matafiya biyu da taron jama’a ya yi musu bayan an yi musu kuskuren zargin su da kasancewa ɓarayi a Ƙaramar Hukumar Igabi ta jihar.
An bayyana sunayen mamatan da Muhammadu Sani da abokin sa Aliyu Mohammed, dukkan su daga ƙauyen Umar da ke Ƙaramar Hukumar Igabi.
Rahotanni sun ce matafiyan suna kan hanyar su ta zuwa Tudun Wada a Zariya domin duba kawun su da ke kwance yana jinya, suna tafiya ne kan wani babur da suka saya kwanan nan, lokacin da aka kai musu hari.
A cewar wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ya fitar, an yi wa mutanen biyun ƙage da cewa ɓarayi ne, inda taron jama’a ya lakaɗa musu duka har suka mutu duk da cewa suna ta bayyana cewa ba su da wani laifi.
‘Yan sanda sun ce jami’an su daga Sashen ‘Yan Sanda na Birnin Yero sun gaggauta kai ɗauki bayan samun rahoton lamarin, inda suka kama mutum shida da ake zargi da hannu a wannan aika-aika.
Sanarwar ta ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun amsa cewa suna da hannu a laifin, kuma a halin yanzu suna tsare a hannun ‘yan sanda, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano tare da kama sauran mutanen da suka shiga wannan kisan ba bisa ƙa’ida ba.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, Rabi’u Muhammad, ya yi Allah-wadai da abin da taron jama’ar suka aikata, tare da yin alƙawarin cewa duk wanda aka samu da hannu a wannan laifi, ba za a yi la’akari da matsayin sa ko muƙamin sa ba, za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kotu bisa tanadin doka.
Ya gargaɗi jama’a da su guji ɗaukar doka a hannun su, yana mai jaddada cewa yin abin da ake kira jungle justice bisa zargi kawai babban laifi ne.
Kwamishinan ya bayyana cewa babu wani mutum da doka ta ba ikon zama mai bincike, alƙali kuma mai aiwatar da hukunci a lokaci guda, yana mai tunatar da jama’a cewa bisa doka, ana ɗaukar duk wanda ake zargi a matsayin mara laifi har sai kotu mai hurumi ta tabbatar da laifin sa.
Ya kuma buƙaci al’umma da su riƙa kai rahoton waɗanda ake zargi da aikata laifi zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko sauran hukumomin tsaro domin gudanar da bincike da gurfanar da su bisa doka, maimakon ɗaukar doka a hannun su.






