Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da kisan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, wanda wasu ’yan bindiga da ke kan babura suka kashe a garin Dutsin-ma da ke Jihar Katsina.
An kashe malamin ne a daren yau Litinin, lokacin da ya fito daga gidan sa domin zuwa gabatar da wa’azin da ya saba yi da yamma, kamar yadda ƙungiyar ta bayyana a cikin wata sanarwa.
Amnesty International ta bayyana kisan a matsayin mummunan aika-aika, tare da kira ga hukumomin Nijeriya da su gudanar da cikakken bincike mai inganci kan lamarin cikin gaggawa.
Ƙungiyar ta buƙaci hukumomi su tabbatar da cewa an gurfanar da duk wanda ake zargi da hannu a kisan gaban kotu domin ya fuskanci hukunci bisa doka.
Ta bayyana cewa Sheikh Masussuka ya kasance yana amfani da wa’azinsa wajen inganta haɗin kai, zaman lafiya, tattaunawa tsakanin mabiya addinai daban-daban da kuma fahimtar juna a tsakanin al’ummar Musulmi.
Marigayin ya kuma yi fice wajen yin wa’azi kan illolin tsattsauran ra’ayi da kuma hana yaɗuwar akidun da ke ƙarfafa tashin hankali.
Amnesty ta ƙara bayyana cewa Sheikh Masussuka ya fuskanci barazanar kisa da tsoratarwa a tsawon rayuwar sa.
Allah-wadan a ƙungiyar ta yi kan kisan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara yin kira da a tabbatar da adalci da kuma inganta tsaron malaman addini da ke ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da zaman tare a cikin al’ummomin su.






