Hajiya Asiya El-Rufai, matar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ta roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar an yi wa mijin ta adalci tare da ba shi damar cin gajiyar haƙƙoƙin da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya tanadar wa kowane ɗan ƙasa yayin da yake fuskantar shari’a.
A lokacin da take magana da manema labarai a gidan su da ke Abuja yau Talata, Asiya ta ce iyalan su ba sa roƙon Shugaban Ƙasa ya tsoma baki cikin shari’ar ko ya dakatar da gurfanar da tsohon gwamnan, sai dai ta buƙaci a ba shi damar samun kulawar lafiya, ganawa da lauyoyin sa da ‘yan’uwan sa, tare da ba shi beli bisa sharuɗɗan da suka dace.
Ta yi wannan kira ne yayin da take martani kan kama likitan Malam El-Rufai, Farfesa Bello Abubakar, matakin da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaƙa (ICPC) ta tabbatar ya faru.
Tare da ɗaya matar El-Rufai, Aichatou, Asiya ta yi zargin cewa an hana mijin ta, wanda aka ce yana fama da hawan jini da kuma hauhawar sikarin jini, samun isasshiyar kulawar lafiya tun bayan tsare shi.
Da take tunatar da irin goyon bayan da iyalan su suka ba Bola Tinubu a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, ta roƙi Shugaban da ya nuna tausayi.
Ta ce, “Mai Girma Shugaban Ƙasa, na yi muku yaƙin neman zaɓe a faɗin Jihar Kaduna. Miji na ya tsaya tsayin daka yana mara muku baya. Shin wannan ne irin sakayyar da iyalan mu suka cancanta?”
Ta jaddada cewa abin da iyalan su ke nema kawai shi ne a mutunta haƙƙoƙin da Kundin Tsarin Mulki ya ba El-Rufai, ciki har da damar samun kulawar lafiya da kuma beli mai sauƙin cikawa.
Ta ce, “Idan yana da laifi, kotu ce za ta yanke hukunci. Idan kuma ba shi da laifi, kotu ce ma za ta tabbatar da hakan. Abin da kawai muke nema shi ne a ba shi damar cin gajiyar haƙƙoƙin da Kundin Tsarin Mulki ya tanada.”
Asiya ta kuma yi zargin cewa tsawaita tsare El-Rufai, da taƙaita masa damar ganawa da ‘yan’uwan sa da lauyoyin sa da likitocin sa, tare da rahotannin cewa an hana likitan sa na ƙashin kan sa ganin sa, sun jefa iyalan su cikin matsananciyar damuwa.
Ta bayyana halin da ake ciki a matsayin wata hanyar matsin lamba ta tunani da ake yi wa tsohon gwamnan da kuma iyalan sa.
Matar tsohon gwamnan ta kuma nuna shakku kan rahotannin da ke cewa an hana Farfesa Bello Abubakar ganin El-Rufai bisa umurnin wasu jami’ai da ba a bayyana sunayen su ba, tana tambayar wanda ya ba da irin wannan umurni.
Har ila yau, ta bayyana damuwa kan wani rahoton lafiya da ake zargin Babban Asibitin Ƙasa da ke Abuja ya fitar, inda ta buƙaci a gudanar da bincike kan sahihancin sa da kuma yadda aka fitar da shi.
A cewar iyalan, takunkumin da aka sanya wa El-Rufai ya sa yana fuskantar ƙalubale wajen shirya kariyar sa a gaban kotu yadda ya kamata.
Sun jaddada cewa ba sa neman a fifita shi fiye da kowa, sai dai suna neman a yi masa shari’a cikin adalci tare da cikakken mutunta haƙƙoƙin da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya tanadar wa duk wani ɗan ƙasa da ke fuskantar tuhuma.







