Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Zamba ta Ƙasa (EFCC) ta samu nasarar hukunta wani mutum mai suna Ali Baffa bisa ƙoƙarin yin sumogar zinari mai nauyin kilogiram 22.2, wanda darajar sa ta haura naira biliyan 4.4, daga Nijeriya.
Hukumar ta bayyana cewa Mai Shari’a Sale Musa Shuaibu na Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ne ya yanke wa Baffa hukunci tare da bayar da umurnin ƙwace zinaren da aka kama zuwa hannun Gwamnatin Tarayya.
An kama Baffa ne a ranar 11 ga Yuni, 2026, lokacin da jami’an EFCC na shiyyar Kano suka cafke shi a ɓangaren zirga-zirgar jiragen sama na ƙasa da ƙasa na filin jirgin saman Malam Aminu Kano.
A cewar hukumar, bincike ya nuna cewa wanda ake tuhuma ya ɓoye sandunan zinari da ba a sarrafa ba, masu nauyin kilogiram 22.2 a jikin sa, domin kauce wa binciken jami’an tsaro.
EFCC ta ce Baffa ya yi niyyar miƙa zinaren ga wasu fasinjoji domin su fitar da shi zuwa Dubai, cikin Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), ba bisa ƙa’ida ba.
Hukumar ta bayyana hukuncin a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa yaƙin da take yi da safarar ma’adanai masu daraja ba bisa ƙa’ida ba da kuma kare albarkatun tattalin arzikin Nijeriya.





