A ci gaba da rangadin ‘Gani Ya Kori Ji’ da Ofishin Babban Mai Taimakawa wa Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Malam Abdulaziz Abdulaziz, ya shirya wa masu aikin jarida, tawagar ta kai ziyara cibiyar Sustainable and Emerging Technology Development Institute (SETDI) da hukumar NASENI take ginawa a sabuwar harabar Jami’ar Bayero, Kano (BUK).
Ziyarar ta bai wa mahalarta damar gani da ido kan ɗaya daga cikin manyan ayyukan Gwamnatin Tarayya da aka ƙaddamar domin bunƙasa kimiyya, fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire a Nijeriya.
A yayin ziyarar, jami’an da ke kula da aikin sun yi wa tawagar cikakken bayani kan yadda cibiyar za ta zama matattarar horas da matasa a fannonin fasahohin zamani da suka haɗa da fasahar AI (Artificial Intelligence), na’urori masu sarrafa kan su (Robotics), makamashi mai ɗorewa da sauran sababbin fasahohi da ke sauya tattalin arzikin duniya.
Sun bayyana cewa aikin yana daga cikin dabarun gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na gina tattalin arziki mai dogaro da ilimi, fasaha da ƙwarewar matasa.
Ziyarar ta ƙara wa manema labarai fahimta kan irin ƙoƙarin da gwamnatin take yi wajen shimfiɗa tubalin ci gaban ƙasa ta hanyar zuba jari a ilimi, bincike da fasahar zamani, bayan da shirin na ‘Gani Ya Kori Ji’ ya ba su damar tantance ayyukan gwamnati kai tsaye domin isar da sahihan bayanai ga al’umma.
Kammala aikin wannan cibiyar zai kasance ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin bincike da bunƙasa fasaha a Afrika, tare da samar da ingantattun ɗakunan gwaje-gwaje, cibiyoyin ƙirƙire-ƙirƙire da horar da matasa, abin da ake sa ran zai ƙara haɓaka masana’antu, samar da ayyukan yi da kuma jawo masu zuba jari zuwa Nijeriya.







