Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da wasu sababbin zarge-zarge da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Mista Peter Obi, ya yi cewa Gwamnatin Tarayya tana bibiyar sa, tana mai bayyana iƙirarin a matsayin ƙarya, yaudara kuma marar wata hujja ingantacciya.
A cikin wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a Abuja yau Laraba, ya ce zarge-zargen Obi, ciki har da iƙirarin cewa motar sa ta samu matsala a filin jirgin sama sakamakon matakin gwamnati, ba su da tushe.
A cewar Onanuga, lamarin da ya shafi motar Obi, kamar yadda tsohon gwamnan Jihar Anambra da kan sa ya bayyana, yana iya kasancewa sakamakon karya ƙa’idojin ajiye motoci na filin jirgin sama, ba wai wata musgunawa daga gwamnati ba.
Hadimin shugaban ƙasar ya kuma yi watsi da iƙirarin Obi cewa wataƙila ba zai kasance a raye ba domin halartar babban zaɓen shekarar 2027, da kuma cewa ana hana mutane gayyatar sa zuwa tarukan zamantakewa.
Ya bayyana waɗannan zarge-zarge a matsayin ƙagaggu da aka ƙirƙira domin jawo tausayin jama’a tare da karkatar da hankali daga abin da ya bayyana a matsayin ƙalubalen da ke fuskantar tafiyar siyasar Obi.
Onanuga ya yi watsi da zargin cewa Gwamnatin Tarayya tana ƙoƙarin takura wa Fidelity Bank saboda alaƙar Obi da bankin.
Ya ce bankin yana ci gaba da samun kyakkyawan cigaba ƙarƙashin sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin da ake ciki, yana mai jaddada cewa gwamnati ba ta da wani dalili na hana bankin gudanar da harkokin sa yadda ya kamata.
Mai magana da yawun Shugaban Ƙasar ya ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tana ci gaba da mayar da hankali kan aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki, kuma ba ta da lokaci ko sha’awar kaucewa daga aikin ta saboda abin da ya kira “labaran da Obi ke ƙirƙira domin amfanin kan sa.”
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da mayar da hankali kan manufofin da za su inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, maimakon mayar da martani ga abin da ya bayyana a matsayin zarge-zarge marasa tushe.







