Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa aikin gina titin Zariya–Funtuwa–Gusau–Sakkwato zai kawo gagarumin sauyi a harkokin sufuri, kasuwanci da tattalin arziki a Arewacin Nijeriya, tare da samar da dubban guraben ayyukan yi da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin jihohin yankin.
An bayyana hakan ne a yau Laraba yayin da tawagar manema labarai da ke cikin shirin ‘Gani Ya Kori Ji’, tare da Babban Mai Taimaka wa Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Malam Abdulaziz Abdulaziz, suka kai ziyara sashe na farko na aikin, wato ɓangaren Zariya–Funtuwa–Sheme, domin duba yadda ake gudanar da aikin.
Jami’an da ke kula da aikin sun shaida wa tawagar cewa titin yana daga cikin manyan ayyukan ababen more rayuwa da gwamnatin tarayya ta bai wa fifiko saboda muhimmancin sa wajen bunƙasa tattalin arzikin Arewa.
Sun bayyana cewa duk da cewa an amince da aikin tun a zamanin gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta inganta shi ta hanyar mayar da shi daga hanya mai layi ɗaya zuwa babbar hanya mai layuka biyu (dual carriageway), domin dacewa da yawan zirga-zirgar ababen hawa da kuma biyan buƙatun ci gaban yankin.

A cewar su, idan aka kammala aikin, titin zai haɗa jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara da Sakkwato cikin sauƙi, tare da inganta zirga-zirgar matafiya da jigilar amfanin gona, dabbobi da sauran kayayyakin kasuwanci.
Sun ƙara da cewa aikin ya haɗa da sake gina titin gaba ɗaya, faɗaɗa shi zuwa layuka biyu, gina sababbin gadoji, magudanan ruwa da kuma girke kayayyakin tsaro na zamani domin rage haɗurran hanya, sauƙaƙa tafiye-tafiye da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Jami’an aikin sun kuma bayyana cewa tun kafin a kammala aikin ya riga ya samar da dubban guraben ayyukan yi ga injiniyoyi, masu sana’o’in hannu, direbobin injuna da sauran ma’aikata daga yankunan da aikin ya ratsa.
Sun ce ana sa ran kammala aikin zai rage kuɗaɗen sufuri, ƙara yawan kasuwanci tsakanin jihohi, jawo masu zuba jari da kuma bunƙasa tattalin arzikin Arewa maso Yamma da Nijeriya baki ɗaya.
Da yake jawabi bayan rangadin, tawagar manema labaran da ke cikin shirin ‘Gani Ya Kori Ji’ ta ce ziyarar ta ba su damar gani da ido kan yadda ake aiwatar da manyan ayyukan gwamnatin tarayya.
A cewar su, aikin titin Zariya–Funtuwa–Sheme na daga cikin muhimman ayyukan da ke nuna ƙudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na aiwatar da Ajandar Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda) ta hanyar inganta ababen more rayuwa, bunƙasa tattalin arziki da kyautata rayuwar al’ummar Nijeriya.







