A ci gaba da rangadin ‘Gani Ya Kori Ji’ na manyan ayyukan gwamnatin tarayya a Arewacin Nijeriya, tawagar manema labarai da ke zagayawa tare da Babban Mai Taimaka wa Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Malam Abdulaziz Abdulaziz, ta kai ziyara zuwa aikin titin Western Bypass domin tantance yadda ake gudanar da shi tare da samun bayanai kai-tsaye daga jami’an da ke kula da shi.
A yayin ziyarar, jami’an kamfanin Sanford Industry Limited, mai aiwatar da aikin, sun bayyana cewa aikin ya zarce kashi 50 cikin 100 na kammaluwa.
Suka ce ana ci gaba da aiki a sassa daban-daban na titin cikin sauri, sakamakon samar da isassun kuɗaɗen gudanar da aikin da gwamnatin tarayya ta yi.
A cewar su, an bayar da kwangilar aikin ne a shekarar 2021, yayin da aka fara aiwatar da shi a shekarar 2023. Aikin ya ƙunshi gina titin mai layuka biyu da tsawon kilomita 21.5, wanda jimillar shimfiɗar kankaren sa ta kai kusan kilomita 43. Haka kuma, aikin ya haɗa da gina gadojin matafiya a ƙafa guda takwas domin kare rayuka da inganta tsaron masu amfani da hanyar.

Jami’an aikin sun kuma bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sake duba kuɗin kwangilar domin ya dace da sauye-sauyen tattalin arzikin ƙasa. Sun ce wannan mataki ya taimaka wajen hanzarta aiwatar da aikin, tare da ba su tabbacin cewa za a kammala shi cikin wa’adin da aka tsara idan aka ci gaba da samun irin wannan goyon baya.
A cewar manema labaran da ke cikin shirin ‘Gani Ya Kori Ji’, aikin titin Western Bypass yana daga cikin manyan ayyukan da za su sauya fasalin zirga-zirga a Jihar Kaduna.
Sun bayyana cewa idan aka kammala shi, zai rage cunkoson ababen hawa a cikin birnin Kaduna, ya sauƙaƙa safarar kayayyaki da zirga-zirgar matafiya, tare da ƙarfafa harkokin kasuwanci da bunƙasa tattalin arzikin jihar da ma yankin Arewa baki ɗaya.
Tawagar ta bayyana cewa cigaban da aka samu a aikin ya nuna yadda gwamnatin Tinubu take ci gaba da aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa a faɗin ƙasar nan, a ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda), da nufin inganta rayuwar al’umma da ƙarfafa cigaban tattalin arzikin Nijeriya.








