• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Mahanga

Dalilin da ya sa Nijeriya take buƙatar ’yan sandan jihohi da yadda doka za ta hana amfani da su ba daidai ba

ALIYU SAMBA by ALIYU SAMBA
July 8, 2026
in Mahanga
A A
0
Dalilin da ya sa Nijeriya take buƙatar ’yan sandan jihohi da yadda doka za ta hana amfani da su ba daidai ba
Jami'an 'yan sanda a wurin wani taro

Jami'an 'yan sanda a wurin wani taro

Yayin da matsalar tsaro take ci gaba da ƙamari a sassa daban-daban na Nijeriya, batun kafa ’yan sandan jihohi (State Police) ya sake zama babban abin tattaunawa. Tsawon shekaru, masana da masu ruwa da tsaki sun yi nuni da cewa rundunar ’yan sandan tarayya kaɗai ba za ta iya ɗaukar nauyin tsaron ƙasa mai jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya ba. A saboda haka ne gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Majalisar Tarayya suke aiki kan gyaran kundin tsarin mulki da kuma samar da dokar da za ta ba da damar kafa tsarin ’yan sanda biyu, wato na tarayya da na jihohi.

Sai dai duk da amincewar da mutane da dama suka nuna da wannan tsari, wasu na nuna damuwa cewa gwamnoni na iya amfani da rundunar ’yan sandan jihohi wajen musguna wa abokan hamayyar su ko tauye haƙƙin jama’a. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya ce an yi la’akari da wannan fargaba tun lokacin da ake tsara ƙudirin dokar, kuma an saka tanade-tanade da za su hana duk wani gwamna amfani da rundunar ba bisa doka ba.

A cewar sa, ɗaya daga cikin manyan matakan kariya da ƙudirin ya tanada shi ne bai wa Shugaban Ƙasa ikon karɓe gudanar da aikin rundunar ’yan sandan kowace jiha idan aka tabbatar tana aiki ta hanyar da ke barazana ga tsaron ƙasa, haɗin kan tarayya ko kuma take amfani da ikon ta wajen karya doka.

A irin wannan yanayi, Shugaban Ƙasa zai iya umurtar Rundunar ’Yan Sandan Tarayya ta karɓe aikin rundunar jihar nan take domin dawo da doka da oda.

Sanata Barau ya kuma bayyana cewa gwamna ba zai kasance da cikakken ikon naɗa kwamandan rundunar ’yan sandan jihar sa yadda ya ga dama ba. A ƙarƙashin ƙudirin, naɗin Kwamandan Rundunar ’Yan Sandan Jiha zai kasance ne bisa shawarar Majalisar Ƙasa kan Harkokin ’Yan Sanda (National Police Council), wadda ta haɗa da Shugaban Ƙasa, gwamnonin jihohi, Sufeto Janar na ’Yan Sanda da tsofaffin manyan jami’an ’yan sanda. Wannan tsari, a cewar sa, zai tabbatar da ƙwarewa, gaskiya da kuma sa ido kan yadda ake tafiyar da rundunar.

A zahiri, kafa ’yan sandan jihohi tana da matuƙar muhimmanci idan aka yi la’akari da irin ƙalubalen tsaro da Nijeriya take fuskanta a yau. Matsalolin ta’addanci, garkuwa da mutane, fashi da makami, rikice-rikicen manoma da makiyaya da sauran laifuffuka na buƙatar jami’an tsaro da suka san al’ummar su, yaren yankin, al’adun su da yanayin wuraren da suke aiki. Irin wannan kusanci da al’umma yana taimakawa wajen tattara sahihan bayanan sirri cikin gaggawa da kuma daƙile laifuffuka kafin su auku.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan ya ce Majalisar Tarayya da gwamnatin Shugaba Tinubu sun gudanar da zaman sauraron ra’ayoyin jama’a a shiyyoyin ƙasar domin tattara shawarwari daga gwamnoni, ƙungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki kafin a kai ga wannan mataki. Ya bayyana cewa akwai cikakkiyar aniyar ganin an samar da tsarin da zai ƙarfafa tsaron ƙasa tare da kiyaye dimokiraɗiyya da haƙƙin jama’a.

Idan aka amince da dokar, za ta ƙara yawan jami’an tsaro a faɗin ƙasar nan, ta kusantar da tsaro ga al’umma, ta inganta tattara bayanan sirri da kuma saurin kai ɗauki a lokacin da ake buƙata. Haka kuma, tanade-tanaden da ke bai wa Shugaban Ƙasa ikon sa baki idan aka samu karkatar da rundunar, da kuma tsarin sa ido na Majalisar Ƙasa kan Harkokin ’Yan Sanda, na daga cikin matakan da aka tanada domin tabbatar da cewa manufar kafa ’yan sandan jihohi ita ce ƙarfafa tsaron Nijeriya, ba wai bai wa wani damar cin zarafin jama’a ko amfani da hukuma don murƙushe abokan hamayya ba.

Tags: 'yan sandatsaro
Previous Post

Tinubu ya ƙaddamar da kwamitin da zai tsara dokar aiwatar da ’yan sandan jihohi

Next Post

Sojoji sun ceto mutanen da aka sace, sun daƙile harin ISWAP, sun kama masu kai wa ‘yan ta’adda kayan aiki a Arewa-maso-gabas

Related Posts

Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’id
Mahanga

Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’id

August 23, 2026
Gwamna Mohammed Umaru Bago: Maraba da Bayyanar Sabon Tauraron Arewa
Mahanga

Gwamna Mohammed Umaru Bago: Maraba da Bayyanar Sabon Tauraron Arewa

July 22, 2026
Illolin Kallon Finafinan Batsa A Addini Da Kimiyya
Mahanga

Illolin Kallon Finafinan Batsa A Addini Da Kimiyya

July 21, 2026
Aikin sake gina titin Abuja–Kaduna ya kai kashi 85% na kammaluwa – Gwamnati
Mahanga

Yadda Shirin ‘Gani Ya Kori Ji’ ya Sauya Zancen Ayyukan Gwamnatin Tarayya a Arewa

July 13, 2026
Abubuwa Goma Da Suke Kawo Damuwa
Mahanga

Abubuwa Goma Da Suke Kawo Damuwa

July 7, 2026
Rayuwa: Kaɗan Daga Cikin Labarin Halin Rayuwar Da Nake Ciki Da Kuma Matsaya Ta A Siyasar 2027 – Umar Tata
Mahanga

Rayuwa: Kaɗan Daga Cikin Labarin Halin Rayuwar Da Nake Ciki Da Kuma Matsaya Ta A Siyasar 2027 – Umar Tata

April 10, 2026
Next Post
Sojoji sun ceto mutanen da aka sace, sun daƙile harin ISWAP, sun kama masu kai wa ‘yan ta’adda kayan aiki a Arewa-maso-gabas

Sojoji sun ceto mutanen da aka sace, sun daƙile harin ISWAP, sun kama masu kai wa 'yan ta'adda kayan aiki a Arewa-maso-gabas

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!