Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, ta ce dakarun ta sun sake samun gagarumar nasara a ayyukan da suke gudanarwa a yankin, inda suka ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su, suka daƙile harin da ake zargin mayaƙan ISWAP ne suka kai, suka kama waɗanda ake zargin suna kai wa ‘yan ta’adda kayan tallafi, tare da ƙwato makamai, alburusai da sauran kayayyaki.
Rundunar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a ranar Laraba.
A cewar sanarwar, dakarun Bataliya ta 115 sun ceto mutum biyu da aka yi garkuwa da su a wani samame na bincike da ceto da suka gudanar ranar 7 ga Yuli a Ƙaramar Hukumar Askira/Uba ta Jihar Borno.
Dakarun sun kuma ƙwato Naira miliyan 1.2 da ake zargin kuɗin da aka samu ne daga ayyukan ta’addanci, tare da kayan abinci da sauran kayayyakin da ake kyautata zaton ana amfani da su wajen tallafa wa ayyukan ‘yan ta’adda.
An kai mutanen da aka ceto zuwa wuri mai tsaro, inda suke samun kulawar likitoci da kuma taimakon rage raɗaɗin abin da ya same su.

A wani samame daban, dakarun da ke Forward Operating Base (FOB) Logomani a Ƙaramar Hukumar Ngala ta Jihar Borno sun samu nasarar daƙile wani hari da mayaƙan ISWAP da ake zargi suka kai.
Sojojin sun ce maharan sun samu damar kutsawa ta wani ɓangare na katangar tsaron sansanin bayan fafatawar da aka yi mai tsanani, amma daga bisani dakarun suka sake haɗa ƙarfi, suka kai martani wanda ya tilasta wa maharan ja da baya bayan sun yi asara mai yawa.
Sai dai, soja ɗaya ya rasu a yayin gumurzun, yayin da motoci biyu na yaƙi da wasu kayan aikin soja suka lalace.
Sanarwar ta ƙara da cewa sansanin yana ci gaba da kasancewa ƙarƙashin ikon dakarun Operation Hadin Kai, kuma an tura ƙarin dakaru tare da ci gaba da gudanar da hare-haren bibiya.

A wani wuri kuma, dakarun Bataliya ta 232, bayan samun sahihan bayanan sirri, sun kama wani fitaccen mutum da ake zargin mai aikata manyan laifuka ne a Ƙaramar Hukumar Gombi ta Jihar Adamawa.
Binciken da aka ci gaba da yi ya kai ga ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, magazin biyu da harsasai 28 nau’in milimita 7.62.
Ana ci gaba da tsare wanda ake zargin a hannun soja yayin da bincike ke gudana.
A Ƙaramar Hukumar Mobbar ta Jihar Borno kuwa, dakarun Bataliya ta 149 sun kama mutum biyu da ake zargin suna kai wa ‘yan ta’adda kayan tallafi.
An ƙwato kuɗi, mota ƙirar Baswaja Golf, kayan gini, kayan amfanin gida da sauran kayayyakin da ake kyautata zaton an tanade su ne domin kai wa ƙungiyoyin ‘yan ta’adda.
Haka zalika, dakarun Birged ta 24 tare da haɗin gwiwar membobin Civilian Joint Task Force (CJTF) sun gudanar da aikin kakkaɓe ‘yan ta’adda a yankin Wulgo, inda suka gano buhun da ke ɗauke da nau’o’in miyagun ƙwayoyi daban-daban da ‘yan ta’addar da suka tsere suka bari.
Rundunar ta kuma bayyana cewa mutum shida da ake zargin membobin ISWAP ne sun miƙa wuya ga dakarun Bataliya ta 192 a Sashen Ɗaya tare da iyalan su.
Binciken farko ya nuna cewa sun tsere ne daga maɓoyar ‘yan ta’adda da ke Guduf Bubayagwa da Chikide a tsaunukan Mandara da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza.
Kayayyakin da aka samu a hannun su sun haɗa da kuɗi Naira miliyan 1.541, wayoyin hannu guda biyu da sauran kayayyakin amfanin kan su.
A wani labarin mai alaƙa da wannan, dakarun da ke shingen bincike na Molai sun kama wani da ake zargin mai kai wa ‘yan ta’adda kayan tallafi ne, bayan an same shi yana jigilar ɗimbin magunguna ba tare da izinin da ya dace ba.
A Sashi na Biyu kuma, dakarun Bataliya ta Tankoki ta 233 tare da haɗin gwiwar mafarauta na yankin sun kama wani da ake zargin mai kai wa Boko Haram/ISWAP kayan tallafi ne a Ƙaramar Hukumar Tarmuwa ta Jihar Yobe, yayin da yake jigilar tayoyin babura guda biyar da ake zargin an nufa da su ga ‘yan ta’adda.

Kyaftin Goni ya ce sababbin nasarorin sun nuna irin tasirin ci gaba da kai hare-haren soja, tattara bayanan sirri da kuma haɗin gwiwar hukumomin tsaro wajen tarwatsa hanyoyin samar da kayan tallafi ga ‘yan ta’adda da kuma kare al’ummomin Arewamaso-gabas.
Ya ƙara da cewa Operation Hadin Kai zai ci gaba da gudanar da ayyukan bincike da ceto har sai an haɗa dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su da iyalan su cikin ƙoshin lafiya.
Rundunar ta yi gargaɗi ga duk wanda ke kai wa ƙungiyoyin ‘yan ta’adda kayan abinci, man fetur, kayan gini, hidimar sufuri ko wata irin gudunmawar kayan aiki da ya daina nan take, tana mai jaddada cewa duk wanda aka kama yana taimaka wa ko haɗa kai da ‘yan ta’adda za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kotu bisa tanadin doka.






