• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu ya ƙaddamar da kwamitin da zai tsara dokar aiwatar da ’yan sandan jihohi

Wakilin Mu by Wakilin Mu
July 8, 2026
in Labarai
A A
0
Tinubu ya ƙaddamar da kwamitin da zai tsara dokar aiwatar da ’yan sandan jihohi
Wakilin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wato Shugaban Ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila, tare da membobin Kwamitin Aiki na Shugaban Ƙasa kan Dokar Tsarin Aikin ’Yan Sanda ta Ƙasa bayan ya ƙaddamar da su a Abuja ranar Talata

Wakilin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wato Shugaban Ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila, tare da membobin Kwamitin Aiki na Shugaban Ƙasa kan Dokar Tsarin Aikin ’Yan Sanda ta Ƙasa bayan ya ƙaddamar da su a Abuja ranar Talata

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da Kwamitin Aiki na Shugaban Ƙasa kan Dokar Tsarin Aikin ’Yan Sanda ta Ƙasa (National Policing Bill), domin tsara dokar da za ta ba da damar aiwatar da tsarin ’yan sandan jihohi a faɗin Nijeriya.

Shugaban Ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila, ne ya wakilce shi wajen ƙaddamar da kwamitin a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Ƙaddamar da kwamitin na zuwa ne bayan Majalisar Tarayya ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki na shekarar 2026 da ya tanadi kafa tsarin ’yan sanda biyu, wato ’Yan Sandan Tarayya da kuma ’Yan Sandan Jihohi 36.

Tinubu ya ce duk da cewa gyaran kundin tsarin mulkin ya kafa tubalin wannan tsari, har yanzu ana buƙatar wata cikakkiyar doka da za ta fayyace yadda za a aiwatar da shi a aikace.

A cewar sa, dokar za ta ƙunshi tanade-tanade kan mafi ƙarancin ƙa’idojin aikin ’yan sanda, tantance shirin kowace jiha kafin kafa rundunar ta, haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da jihohi, tabbatar da bin haƙƙin ɗan’adam, ɗaukar nauyin kuɗaɗe da kuma hanyoyin tabbatar da gaskiya da riƙon amana.

Ya ce manufar kwamitin ita ce samar da cikakkiyar daftarin dokar da za a miƙa wa Majalisar Tarayya ba tare da ɓata lokaci ba.

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun, ya tabbatar da cewa gwamnoni za su mara wa shirin baya tare da hanzarta amincewa da gyaran kundin tsarin mulkin a majalisun dokokin jihohin su.

Ya ce tsarin ’yan sandan jihohi zai amsa buƙatar da ’yan Najeriya suka daɗe suna yi ta samar da tsaro mai kusanci da al’umma, ya ƙara da cewa idan kowace jiha ta ɗauki kimanin jami’ai 6,000, za a samu kusan karin jami’an tsaro 200,000 a faɗin ƙasar nan.

Shi ma Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi, ya bayyana shirin a matsayin mataki mai muhimmanci duba da ƙalubalen tsaron da ƙasar ke fuskanta, inda ya buƙaci gwamnoni su tabbatar da amincewa da gyaran kundin tsarin mulki cikin gaggawa.

A nasa ɓangaren, Shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA), Afam Osigwe, ya bayyana goyon bayan ƙungiyar sa ga kafa ’yan sandan jihohi, tare da jaddada buƙatar samar da ingantattun tanade-tanaden doka da za su hana amfani da rundunar wajen tauye haƙƙin jama’a ko cin zarafi.

Tags: 'yan sandan jihohiFemi GbajabiamilaShugaba Bola Ahmed Tinubu
Previous Post

Gani Ya Kori Ji: Sabuwar cibiyar NASENI ta BUK za ta zama matattarar horas da matasa kan fasahohin ƙarni na 21

Next Post

Dalilin da ya sa Nijeriya take buƙatar ’yan sandan jihohi da yadda doka za ta hana amfani da su ba daidai ba

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Dalilin da ya sa Nijeriya take buƙatar ’yan sandan jihohi da yadda doka za ta hana amfani da su ba daidai ba

Dalilin da ya sa Nijeriya take buƙatar ’yan sandan jihohi da yadda doka za ta hana amfani da su ba daidai ba

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!