A siyasa, ba sabon abu ba ne a samu saɓanin ra’ayi tsakanin masu mulki da ‘yan adawa. Amma duk lokacin da aka yi zance kan ci gaban ƙasa, abin da ya fi muhimmanci shi ne hujja. Wannan ne ya sa ƙaddamar da shirin Gani Ya Kori Ji ya zo a daidai lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatar da ayyukan raya ƙasa, musamman a Arewacin Najeriya.
Tun bayan hawan gwamnatin Tinubu, ɗaya daga cikin zarge-zargen da aka fi maimaitawa shi ne cewa yankin Arewa ba ya samun rabon ayyukan raya ƙasa yadda ya kamata. Wannan zargi ya mamaye kafafen yaɗa labarai da shafukan sada zumunta har ya fara zama tamkar abin da mutane da dama suka amince da shi ba tare da bincike ba.
Sai dai abin da shirin Gani Ya Kori Ji ya yi shi ne mayar da martani ta hanyar da ta fi kowace magana ƙarfi, wato kai jama’a zuwa inda ayyukan suke gudana domin su gani da idanunsu.
Yawon ya zagaya wasu muhimman ayyukan gwamnatin tarayya da suka haɗa da Abuja Independent Power Project, titin Abuja–Kaduna–Kano, aikin AKK Gas Pipeline, Kano Northern Bypass, layin dogo na Kano–Maradi, cibiyoyin lafiya, ayyukan ban ruwa, makamashin hasken rana, shirye-shiryen amfani da iskar gas ta CNG da sauran manyan ayyukan more rayuwa.
Abin lura shi ne, wannan yawon bai ba masu sukar gwamnati mamaki kaɗai ba. Har ma wasu daga cikin masu goyon bayan gwamnati sun bayyana mamakinsu da irin yawan ayyukan da suka gani. Dalili kuwa shi ne, yawan ce-ce-ku-cen siyasa ya sa har masu goyon bayan gwamnati ba su da cikakken bayani kan yawancin ayyukan da ake aiwatarwa a yankin Arewa.
Wannan ya nuna wani babban darasi a fannin sadarwa. Ba koyaushe rashin aiki ne matsala ba, wani lokaci rashin isar da sahihin bayani ne ke barin gurbi da jita-jita ke cikewa. Idan gwamnati ta kasa bayyana abin da take yi, wasu za su cike wannan gibi da nasu labarin.
A nan ne Gani Ya Kori Ji ya nuna muhimmancinsa. Ya sauya salon tattaunawa daga musun siyasa zuwa hujja. Titin da aka shimfiɗa, gadar da ake ginawa, layin dogo, bututun iskar gas, tashar wutar lantarki ko asibitin da ake ginawa ba sa buƙatar doguwar muhawara. Ana iya zuwa a gani, a duba ci gaban da aka samu, sannan a yanke hukunci bisa abin da ido ya gani.
Bayanan da hukumomin gwamnati suka fitar sun nuna cewa yankin Arewa maso Yamma na daga cikin yankunan da ke da mafi yawan ayyukan gwamnatin tarayya, musamman a bangaren manyan hanyoyi, layukan dogo, makamashi, lafiya da noma. Wannan ba yana nufin an kammala komai ba ne, ko kuma babu wuraren da ya kamata a ƙara himma. A’a. Ayyukan ci gaba suna buƙatar lokaci, kuma gwamnati tana da alhakin tabbatar da cewa an kammala su cikin inganci da lokacin da aka tsara.

Sai dai abin da wannan yawon ya tabbatar shi ne cewa muhawarar da ta shafi rabon ayyuka ya kamata ta kasance bisa hujjoji da bayanai, ba bisa hasashe ko ra’ayin siyasa kawai ba.
Abin farin ciki shi ne, shirin bai tsaya a jihohin da aka kai ba. An tsara shi ne domin ya zagaya dukkan jihohin Arewacin Najeriya, inda za a ci gaba da nuna manyan ayyukan da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa. Wannan zai ba jama’a damar yin hukunci bisa abin da suka gani da kansu, ba abin da suka ji kawai ba.
A ƙarshe, darasin da Gani Ya Kori Ji ya koyar shi ne cewa a dimokiraɗiyya, suka na da muhimmanci, amma sukar da tafi amfani ita ce wadda ta ginu a kan hujjoji. Haka kuma, gwamnati ba ta isa ta aiwatar da aiki kawai ba, dole ne ta tabbatar jama’a sun san abin da take yi.
Domin a ƙarshe dai, kamar yadda karin maganar Hausawa ke cewa, gani ya kori ji.







