Bayyanar hasken walƙiya da rugugin ƙarajin sautin muryar Gwamna Mohammed Umar Bago na Jihar Neja, ya zo daidai lokacin da ake tsananin buƙatar samun zaƙaƙurin da zai yi irin wannan gurnani da gumza, wadda amsa-amon ta zai karaɗe Arewacin Nijeriya. Sai kuwa aka yi sa’a sautin ƙarfin muryar ya shiga kunnuwan kowa, na nesa da na kusa, hatta gafalallun da ke kwance suna barcin rashin damuwa da gagarumar matsalar Arewa, sai da sautin muryar Gwamna Bago ya tayar da su daga barci. Dama Bahaushe ya ce, “ko yaro na goye ya san kura. Idan bai san jikin ba, ya san kuka.”
Daga tun da matsalar mummunan tashin hankalin kashe-kashe ya buwayi Arewa maso Yamma har ya kutsa cikin Jihar Neja, ba a taɓa samun wani jajirtaccen da ya fito gaba-gaɗi ya shaida wa jama’a abin da sauran masu iko suka kasa fitowa su furta ba. Babu buƙatar sake nanata abin da Bago ya faɗa, domin muryar sa ta rigaya ta shiga ko’ina. Bago ya nuna ɓacin ran yadda muka lalace ba mu da wani aiki sai kashe junan mu, mu-ya-mu. Mun zama marmara, ci kan ki da kan ki.
Ban yi mamakin irin jarumtar da Bago ya nuna wajen gargaɗin bayyana irin matakan da zai ɗauka a matsayin sa na gwamna ba. Domin idan aka dubi jihar da ta haifi Bago, wato Neja, za a tabbatar da cewa jiha ce da ta haifi manyan baraden Arewa uku a baya, waɗanda har yau ake tutiya da su, tare da cin moriyar ginin da suka yi wa Arewa.
Jihar Neja ta haifi tsohon Shugaban Ƙasa Ibrahim Babangida, gwarzon da ya fito tsakar fagen yaƙi, shi ɗaya tilo, ya tarbi abokan fama. Daga mai sara da takubba, sai masu sukar sa da masu, sai masu cilla masa kibau masu dafi. Amma haka IBB ya jure, sai da ya kinkimo hedikwatar Nijeriya daga Legas ya maido ta Arewa, a Abuja.
Babangida bai tsaya a nan ba, sai da ya ƙara yawan jihohi da ƙananan hukumomi. Kuma ya yi nagartattun ayyuka masu nuna tabbas da bai jure nauyin ɗauko babban birnin tarayya zuwa Abuja ba, to da yanzu ‘yan Arewa ba su yi tasirin da suke da shi a yanzu ba.
Mutumin Neja na biyu mai tasiri a Arewa da Nijeriya kuwa, shi ne tsohon Shugaban Ƙasa Abdulsalami Abubakar, wanda bayan ya hau mulki, sai ya nuna dattakon maido da mulkin dimokiraɗiyya cikin watanni 9 kacal. Duk wani ɗan siyasa a yanzu albarkacin Abdulsalami yake ci, tun daga 1999 har zuwa yau.
Dattakon da ya nuna ne ma ya sa a yanzu ake ganin karsashin dattijantakar tasa fiye da sauran dattawan tsofaffin shugabanni, har ake sa shi shiga-tsakani a duk lokacin da wata dambarwar sha’anin mulki ta kunno kai.
Mutum na uku daga Jihar Neja wanda ya yi tasiri a Arewa, shi ne marigayi Abubakar Imam, wanda ya rasu a cikin 1981. Ya bada gagarumar gudunmawa a fannin bunƙasa harshen Hausa. Ya yi ɗan majalisa, kuma ya riƙe muƙamin Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Arewa.
Yanzu kuma sai muka wayi gari da bayyanar hudowar hasken tauraron wani ɗan Jihar Neja, wanda jarumtar gargaɗi ce kaɗai ya yi, amma ya tashi masu barci, ya fargar da mugaffalai, kuma ya tsima duk wani mai ɗarsashin kishi da ƙaunar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Dama fa irin Gwamna Bago ne aka rasa a Sokoto da Zamfara da Kebbi da Kaduna da Katsina, shi ya sa tashe-tashen hankula da munanan kashe-kashe suka kassara waɗannan jihohi, har balbalin wannan bala’i ya afka Jihar Neja, Abuja, Nassarawa da Benuwai. Mun rasa irin Gwamna Bago shi ya sa lalacewa ta kai maƙura a jihohin Arewa maso Yamma, har lamarin ya yi munin da babu ci gaba sai kisa da bindiga, garkuwa da mutane, yi wa ɗan Adam yankan rago, banka wa dukiyoyin mutanen karkara wuta, tarwatsa manoma, satar shanu, biyan kuɗin fansa da sauran manyan ayyukan ta’addanci.
Harkokin noma sun lalace a Arewa, an tarwatsa yankunan karkara, haka fannin ilmin zamani, saboda babu zaman lafiya a karkara ballantana a samu sukunin zaman samu da bayar da ilmin.
Kasuwancin tsaka-tsaki da ƙananan ‘yan kasuwa ya durƙushe. Lalacewar Arewa ta kai maƙurar da matasan mu sun fantsama cikin ƙasashen Aljeriya, Libiya, Maroko, har cikin ƙasashen Turai irin su Sifaniya.
A nan Nijeriya, dandazon matasa sun tsere wa tashe-tashen hankula, sun guje wa noma a yankunan su, sun nausa Benuwai suna noma, wasu kuma na yin ƙasƙantattun sana’o’in ciyar da kai da ciyar da iyali. Dafifin matasan Arewa na Bayelsa, Legas har cikin jihohin Arewa maso Gabas. Masu gajeren zango ne za ka gani danƙam cikin garuruwan da ke kewaye da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Ganin yadda wannan matsala ke ƙara ƙamari ta sa Gwamna Bago fitowa domin ya tunkare ta gaba gaɗi. Ya fito ƙiriƙiri ya bayyana sabubba da tushen yadda waɗannan matsaloli ke ƙara yin tsiro da toho. Sannan ya bayyana yadda zai magance su. To mene ne laifin Umar Bago? Ya rage wa al’ummar Jihar Neja su haɗa kai su goya masa baya, domin su fita daga cikin wannan matsala. Kuma ya rage wa sauran gwamnonin Arewa su fito su ɗauki salo da samfur ɗin da Gwamna Bago ya ɗauka, domin sauke nauyin haƙƙin da ke wuyan ku.
Magana ta gaskiya, a wannan matsanancin hali da Arewa ke ciki, ba Jihar Neja ce kaɗai ke buƙatar Bago ba. Arewa bakiɗaya na buƙatar sa. Duk kuwa wanda Arewa ke buƙata, to tabbas Nijeriya ɗungurugum tana buƙatar sa.
Muhammadu Umar Bago, gwamna mai shekaru 52 a duniya. Kana da sauran lokacin tunkarar ƙalubale. Sannu da ƙoƙari. Gaishe ka da bayyana gaskiya. Sai dai me? Ya kamata ka fahimci cewa Arewa kaf suna goyon bayan ka. Babu mai ganin aibin ka, daga ‘yan takife sai ‘yan ƙarambosuwa. Ita kuwa ƙarambosuwa shirgin kaya ne, waɗanda ko tattara su aka yi aka sayar, to farashin su ba daraja zai yi ba.
*Ashafa Murnai ɗan jarida ne, mai nazarin harkokin yau da kullum. Imel: ashafamurnai60@gmail.com







