• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Sarkin Musulmi da wakilin Paparoma Sun yi gargaɗi kan rashin haƙurin addini, kalaman ƙiyayya da yaɗa labaran ƙarya

Wakilin Mu by Wakilin Mu
July 7, 2026
in Labarai
A A
0
Sarkin Musulmi da wakilin Paparoma Sun yi gargaɗi kan rashin haƙurin addini, kalaman ƙiyayya da yaɗa labaran ƙarya
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III, yana ganawa da wakilin Paparoma, Achibishop Paul Richard Gallagher da tawagar sa a Abuja 

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III, yana ganawa da wakilin Paparoma, Achibishop Paul Richard Gallagher da tawagar sa a Abuja 

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya yi gargaɗin cewa ƙaruwar rashin haƙurin addini, kalaman ƙiyayya, yaɗa labaran ƙarya da kuma taɓarɓarewar ɗabi’u suna barazana ga haɗin kan Nijeriya da zaman lafiya tsakanin al’umma.

Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake karɓar baƙuncin wakilin Paparoma, Achibishop Paul Richard Gallagher, tare da tawagar sa, a wani taro da aka shirya domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin shugabannin Musulmi da Kiristoci wajen samar da zaman lafiya da bunƙasa ƙasa.

Sarkin Musulmin, wanda Mataimakin Babban Sakataren Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA), Farfesa Salisu Shehu, ya wakilta, ya jaddada muhimmancin ƙara tattaunawa, fahimtar juna da haɗin gwiwa tsakanin mabiya addinan biyu domin magance matsalar tsaro da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Ya bayyana cewa kalaman ƙiyayya suna ci gaba da haifar da rashin amincewa tsakanin mabiya addinai tare da ƙara rarrabuwar kawuna, yayin da yaɗa labaran ƙarya ke ƙara tayar da hankali da haddasa rikice-rikicen da za a iya kauce wa.

Taron na shugabannin addinai yana ci gaba da gudana

Sarkin Musulmin ya kuma yi Allah-wadai da yadda ake cin mutuncin manyan shugabannin addinai, inda ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su riƙa mutunta juna ba tare da la’akari da bambancin addini ko ƙabila ba.

Haka kuma ya nuna damuwar sa kan abin da ya bayyana a matsayin taɓarɓarewar ɗabi’u da kuma ƙin bin koyarwar addinai da ake samu a tsakanin matasa, yana mai kira da a ƙara ba da muhimmanci ga tarbiyyar ɗabi’a da ilimin addini.

Da yake magana bayan taron, Achibishop Gallagher ya bayyana tattaunawar da aka yi da cewa “ta kasance mai gaskiya kuma mai faɗakarwa,” yana mai cewa shugabannin Musulmi da Kiristoci suna da ƙimomi da nauyin da suka yi tarayya a kai wajen inganta zaman lafiya, jituwa tsakanin addinai da cigaban al’umma.

Ya bayyana fatan cewa ci gaba da tattaunawa da haɗin gwiwa tsakanin addinai zai ƙara ƙarfafa haɗin kan ƙasa tare da samar da ɗorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya.

Tags: Achibishop Paul Richard GallagherAlhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar IIIFarfesa Salisu ShehuPaparomaSarkin Musulmitaro
Previous Post

Gwamnati za ta binciki kamfanonin fasaha na duniya kan zargin take haƙƙin kafafen yaɗa labarai na Nijeriya

Next Post

Tinubu ya umurci ICPC da ta binciki ‘hukumar bogi’, ta gabatar da rahoto cikin kwana 30

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Tinubu ya umurci ICPC da ta binciki ‘hukumar bogi’, ta gabatar da rahoto cikin kwana 30

Tinubu ya umurci ICPC da ta binciki 'hukumar bogi', ta gabatar da rahoto cikin kwana 30

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!