• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

UMAR GARBA by UMAR GARBA
November 25, 2026
in Labarai
A A
0
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Sarkin Daura, Alhaji Umar Faroukh da mai zargin sa, Mirka Czee

Sarkin Daura, Alhaji Umar Faroukh da mai zargin sa, Mirka Czee

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin da ta kafa jiya domin gudanar da bincike kan zargin taɓa jikin wata Baturiya ‘yar yawon buɗe ido da ya shafi Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar.

Baturiyar da ta yi zargin, sunan ta Mirka Czee, wadda ‘yar ƙasar Poland ce da aka haifa a Jamhuriyar Czech. Tana amfani da manhajar Instagram da shafi mai suna @beduinqa.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Jihar Katsina, Dakta Bala Salisu Zango, ya faɗa cewa Gwamnan Jihar Katsina, Dakta Dikko Umaru Raɗɗa, ya amince da naɗin waɗannan mutane a matsayin mambobin kwamitin:

1. Mai Shari’a Amiru Sanusi (mai ritaya) – Shugaban Kwamitin.

2. Hon. Usman Abba – Mai Ba Gwamna Shawara na Musamman kan Harkokin Masarautu.

3. Mai Shari’a Sadiq A. Mahuta (mai ritaya), Galadiman Katsina.

4. Hon. Isah Dabai – Kwamishinan Harkokin Addini.

5. Alhaji Lawal Aliyu Daura.

6. Farfesa Halima Kabir Daura – Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.

7. Dakta Bala Salisu Zango – Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar Katsina.

8. Hajiya Khadija Abdulƙadir – Mai Ba Masarautar Belgium Shawara kan Harkokin Diflomasiyyar Tattalin Arziki.

9. Fadila Muhammad Dikko – Mai Girma Babbar Lauya kuma Kwamishiniyar Shari’a ta Jihar Katsina, wadda za ta kasance Sakatariyar Kwamitin.

A cewar sanarwar, kwamitin yana da waɗannan sharuɗɗan gudanar da ayyuka waɗanda za su jagorance shi wajen gudanar da binciken sa:

1. Binciken zargin cin zarafin jima’i da ake yi wa Sarkin Daura.

2. Gayyatar duk mutanen da lamarin ya shafa ko waɗanda suke da alaƙa da zargin.

3. Gano ainihin dalilin ziyarar baƙuwar yawon buɗe ido zuwa fadar Sarkin.

4. Binciken duk wasu takardu, bayanai da hujjoji masu alaƙa da lamarin.

5. Gudanar da duk wasu ayyuka da suka zama dole ko suke da alaƙa da tabbatar da adalci a kan lamarin.

6. Gano irin matsayin alhakin da Sarkin Daura yake da shi dangane da zargin.

7. Ba da shawarar matakan hukunci da suka dace.

8. Ba da shawarar matakan gyara da za su hana sake faruwar irin wannan lamari a nan gaba.

9. Miƙa rahoton binciken sa cikin makonni huɗu daga ranar ƙaddamar da aikin kwamitin.

Ana sa ran kwamitin zai fara gudanar da aikin sa nan take bayan ƙaddamar da shi, sannan ya miƙa rahoton sa cikin wa’adin da aka ƙayyade.

Kwamishinan ya ce gwamnati na kira ga al’umma da su ba kwamitin damar gudanar da aikin sa cikin ’yanci ba tare da matsin lamba marar dacewa ba.

Haka kuma ta buƙaci jama’a da su guji duk wani aiki ko furuci da zai iya kawo cikas ga binciken ko kuma ya shafi gudanar da aikin kwamitin.

Gwamnatin ta kuma tabbatar wa da ’yan ƙasa cewa za a tabbatar da adalci bisa sakamakon binciken da kwamitin zai gabatar.

Tags: Alhaji Umar Faroukh Umarkwamitin bincikeMirka CzeeSarkin Daurazargi
Previous Post

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

Next Post

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC
Siyasa

Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC

November 24, 2026
Next Post
Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

Al'ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!