Hukumar Kula da Gasa da Kare Haƙƙin Jama’a Masu Sayayya ta Tarayya (FCCPC) za ta binciki manyan kamfanonin fasaha na duniya bayan zargin cewa suna aikata halaye masu tauye gasa, yin amfani da labaran kafafen yaɗa labarai ba bisa ƙa’ida ba, da kuma wasu ayyuka da ba su dace da adalcin kasuwanci a Nijeriya ba.
Haka kuma binciken zai shafi dandamalin fasahar ƙirƙire-ƙirƙire (generative Artificial Intelligence, AI) da ke gudanar da ayyuka a Nijeriya.
Daraktan Harkokin Hulɗa da Jama’a na FCCPC, Ondaje Ijagwu, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar manema labarai ranar Litinin, inda ya ce hakan ya biyo bayan umurnin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba hukumar da ta binciki ƙorafin haɗin gwiwa wanda Ƙungiyar Kafafen Yaɗa Labarai ta Nijeriya (NPO) ta miƙa wa Fadar Shugaban Ƙasa.
Ita dai NPO, ta ƙunshi Ƙungiyar Mamallakan Jaridu ta Nijeriya (NPAN), Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), Ƙungiyar Gidajen Rediyo da Talbijin ta Nijeriya (BON), da kuma Ƙungiyar Masu Wallafa Labarai ta Yanar Gizo (GOCOP).
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana matsayar Gwamnatin Tarayya kan al’amarin ga FCCPC ta hanyar wata wasiƙa da ya sanya wa hannu.
Ana sa ran wannan bincike zai buɗe sabon babi a tarihin kafafen yaɗa labarai na Nijeriya. A cikin ‘yan shekarun nan, masana’antar yaɗa labarai ta Nijeriya ta riƙa nuna damuwa kan yadda wasu manyan dandamalin dijital suke yin tasiri ga ɗorewar tsarin samar da labarai a ƙasar nan.
Hasali ma dai, ƙungiyar NPO ta nuna rashin jin daɗin ta da yadda wasu manyan kamfanonin fasaha irin su Meta, Alphabet, X (wanda a da ake kira Twitter), da wasu dandamalan “Generative AI” suke gudanar da ayyukan su.
Ƙungiyar ta ce waɗannan ayyuka suna iya tauye gasa ta gaskiya, su raunana cigaban kasuwancin kafafen yaɗa labarai na Nijeriya, kuma su take haƙƙin masu ƙirƙira da masu wallafa bayanai.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Mataimakin Shugaban Hukumar FCCPC kuma Babban Darakta, Mista Tunji Bello, ya sake jaddada aniyar hukumar ta gudanar da bincike mai zaman kan sa, cikin gaskiya, kuma bisa hujjoji.
Ya ce: “Mun fahimci muhimmancin kafafen yaɗa labarai ga dimokiraɗiyyar Nijeriya, haka kuma mun san irin rawar da fasaha ke takawa wajen bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire da tattalin arziki. Nauyin da ke kan mu shi ne mu tantance gaskiyar abin da ake zargi tare da tabbatar da cewa gasa a cikin tsarin dijital tana gudana cikin adalci, tsare gaskiya, kuma bisa dokokin Nijeriya.”
Bello ya ƙara da cewa: “Ba a fara wannan binciken da zaton cewa wani ya aikata laifi ba. Manufar sa ita ce a binciki gaskiyar lamarin, a saurari dukkan ɓangarorin da abin ya shafa, sannan a tantance ko akwai wasu ayyuka da suka haifar da tauye gasa ko kuma halayen kasuwanci marasa adalci. Za a bai wa kowane ɓangare cikakkiyar dama ya gabatar da bayanan sa kafin a cimma wata matsaya.”
A zahiri, FCCPC za ta bincika ko ayyukan da ake zargi sun saɓa wa Dokar Gasa da Kare Haƙƙin Masu Sayayya ta Tarayya ta shekarar 2018 (FCCPA) ko kuma wata doka da ta dace.
A baya, FCCPC ta taɓa bincikar kamfanin Meta (mamallakin Facebook da WhatsApp da Instagram), kuma a shekarar 2025 ta samu nasara a wata babbar shari’a da aka yi da kamfanin kan karya dokokin FCCPA, ciki har da take sirrin bayanan masu amfani da manhajoji. An ci tarar kamfanin dala miliyan 220, sai dai Meta ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
A sabon binciken, FCCPC za ta mayar da hankali kan batutuwa da dama, ciki har da zargin mamaye kasuwanci da kuma halayen da ke tauye gasa. Haka kuma za ta binciki zargin cirewa, kwafa, tattarawa ko amfani da labaran jaridu, shirye-shiryen rediyo da talbijin da sauran rubuce-rubucen aikin jarida masu kariyar haƙƙin mallaka ba tare da izini ba wajen ƙirƙira da horar da tsarin “Generative AI.”
Bugu da ƙari, binciken zai duba ƙorafin da ke nuna cewa babu adalci a mu’amalar kasuwanci tsakanin manyan kamfanonin fasaha na duniya da masu wallafa labarai na Nijeriya.
Babban abin da ake zargi shi ne cewa kafafen yaɗa labarai da abin ya shafa ba su samun damar tattaunawa domin cimma yarjejeniyar biyan diyya ko wasu tsare-tsaren kasuwanci masu adalci kan yadda ake amfani da labaran su.
Abin lura shi ne, bayan irin wannan ƙorafi da kafafen yaɗa labarai suka gabatar a ƙasar Afrika ta Kudu, da kuma binciken da Hukumar Gasa ta ƙasar ta gudanar, an cimma yarjejeniya inda kamfanin Google ya amince zai riƙa biyan kafafen yaɗa labarai na Afrika ta Kudu rand miliyan 688 (kimanin dala miliyan 40 kenan) a duk shekara na tsawon shekaru uku zuwa biyar.






