Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaƙa, wato ICPC, da ta gudanar da cikakken bincike kan ayyukan hukumar nan da ake kira “Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC)” da kuma duk wasu batutuwa da suke da alaƙa da ita.
Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata cewa Tinubu ya umurci a kammala binciken tare da gabatar masa da cikakken rahoto cikin kwana 30.
Umurnin ya biyo bayan gano cewa PFIPC hukumar bogi ce wadda Gwamnatin Tarayya ba ta taɓa kafawa ba, kuma ba ta da wata madogara a cikin kowace doka, umurnin shugaban ƙasa, amincewar majalisar zartarwa ko wani sahihin matakin gwamnati.
Onanuga ya ce:
“Wani mutum mai suna Adeniyi Adeyemi Matthew ya riƙa gabatar da kan sa a matsayin Darakta Janar na abin da ake kira PFIPC, tare da yin ƙaryar cewa shugaban ƙasa ne ya naɗa shi.”
Ya ce daga cikin batutuwan da ICPC za ta bincika akwai wasiƙun naɗin aiki na bogi da sauran takardun gwamnati da aka ƙirƙira; amfani da ƙaryar cewa shugaban ƙasa ne ya naɗa mutum domin neman ko samun amincewar hukumomi da goyon bayan diflomasiyya, ciki har da samun biza a sauƙaƙe; da kuma buɗe asusun ajiyar kuɗi da dama da sunayen wasu hukumomin gwamnati ta hanyar amfani da takardun da ake zargin an ƙirƙira.
Shugaban Ƙasar ya kuma umurci ICPC da ta binciki ba wai halayen babban wanda ake zargi da sauran abokan haɗin bakin sa kaɗai ba, har ma da yanayin da ya bai wa wata hukuma ta bogi da kuma ƙaryar wai naɗin shugaban ƙasa damar bayyana kamar halastacciyar hukuma ce ta gwamnati.
Onanuga ya ce:
“Binciken zai tantance asali da yadda aka yi amfani da takardun bogi na gwamnati; hanyoyin da aka bi wajen neman ko samun amincewar hukumomi ko goyon bayan diflomasiyya; buɗewa da gudanar da duk wasu asusun banki da ke da alaƙa da lamarin; tushen kuɗaɗen da abin ya shafa da yadda aka sarrafa su; da kuma rawar da duk wani jami’in gwamnati, mutum mai zaman kan sa, cibiyar kuɗi, mai shiga tsakani ko wata hukuma ko ƙungiya ta taka wajen sauƙaƙe ko shiga cikin wannan zargin.”
Shugaban Ƙasar ya kuma umurci hukumar da ta gano duk wata matsala ko rauni da ke cikin tsare-tsaren gwamnati da na hukumomi da aka yi amfani da su wajen aikata wannan zamba, tare da ba da shawarwarin gaggawa domin hana sake aukuwar irin wannan a nan gaba.
Haka kuma, an umurci dukkan ma’aikatu, sassa da hukumomin Gwamnatin Tarayya da su bai wa ICPC duk wani bayani, takardu da haɗin kai da take buƙata bisa doka domin kammala binciken cikin gaggawa.
Tinubu ya jaddada cewa dole ne a kare mutunci da martabar Fadar Shugaban Ƙasa da hukumomin Gwamnatin Tarayya daga masu kwaikwayon jami’ai, masu ƙirƙirar takardun bogi, masu amfani da sunan gwamnati ba bisa ƙa’ida ba, da kuma masu cin gajiyar raunin da ke cikin tsarin aikin gwamnati.
A cewar kakakin shugaban ƙasar, “Shugaban Ƙasa ya umurci cewa duk wanda aka samu da laifi a binciken a hukunta shi da tsauraran matakai bisa tanadin dokokin ƙasa.”







