• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Asusun IMF ya jinjina wa manufofin kuɗi na CBN, ya yaba da shirin ƙarfafa jarin bankuna

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
June 10, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Asusun IMF ya jinjina wa manufofin kuɗi na CBN, ya yaba da shirin ƙarfafa jarin bankuna
Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana cikakken goyon bayan ga tsauraran manufofin kuɗi da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ke aiwatarwa.

Haka kuma IMF ya nuna gamsuwa kan gyare-gyaren da CBN ke yi a fannin bankuna, wato ƙara yawan jarin bankuna. Yana mai bayyana matakan da CBN ya ɗauka a baya-bayan nan a matsayin muhimman hanyoyi na tabbatar da daidaiton tattalin arziki da kuma ƙarfafa amincewa da tattalin arzikin Nijeriya.

A cikin rahoton sa kan Nijeriya na shekarar 2026, wanda aka fitar a ranar Talata, IMF ya yaba wa CBN saboda ci gaba da aiwatar da gyare-gyare masu wahala amma masu muhimmanci, waɗanda suka taimaka wajen daidaita kasuwar canjin kuɗaɗen waje, rage matsin hauhawar farashi da kuma sake gina ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje duk da ci gaba da rashin tabbas a tattalin arzikin duniya.

Sannan kuma IMF ya nuna amincewa da matakan tsaurara manufofin kuɗi da Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ke jagoranta bisa ga bayanan tattalin arziki, yana mai jaddada cewa dole ne a ci gaba da tsaurara manufofin kuɗi har sai an tabbatar da daidaituwar hauhawar farashi.

“Daraktocin IMF sun yaba da nasarar da hukumomi suka samu wajen rage hauhawar farashi,” inji IMF, yayin da ya lura cewa sabon hauhawar farashin makamashi da abinci a duniya suna sake haifar da matsin hauhawar farashi ga tattalin arzikin Nijeriya.

Rahoton ya bayyana cewa hauhawar farashi ta ci gaba da raguwa fiye da shekara guda kafin wasu matsalolin waje da suka samo asali daga rikicin Gabas ta Tsakiya suka sa adadin hauhawar farashin gaba ɗaya ya ɗan tashi zuwa kashi 15.4 cikin ɗari a watan Maris na shekarar 2026.

IMF ya ce ingantaccen adadin ribar manufofin kuɗi na CBN da kuma tsauraran matakan sarrafa yawan kuɗaɗen da ke yawo a tattalin arziki sun ƙarfafa amincewar masu zuba jari tare da inganta sahihancin manufofin kuɗi.

Asusun ya kuma yaba da ci gaban da CBN ya samu wajen rungumar tsarin manufofin da ke mayar da hankali kan sarrafa hauhawar farashi, yana mai bayyana hakan a matsayin babban gyaran hukuma wanda zai inganta sadarwa kan manufofi da kuma ƙarfafa amincewar kasuwa.

IMF ya kuma amince cewa gyare-gyaren da aka yi a kasuwar canjin kuɗaɗen waje sun inganta matsayin Nijeriya a harkokin kuɗaɗen waje.

Rahoton ya nuna cewa jimillar ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje ta ƙaru zuwa dala biliyan 46 a shekarar 2025 daga dala biliyan 40 a ƙarshen shekarar 2024, sakamakon ingantaccen ciniki da ƙasashen waje, ƙaruwar shigowar kuɗaɗe daga waje da kuma amincewar da masu zuba jari suka yi wa sabuwar alƙiblar manufofin kuɗi.

Haka kuma, ajiyar kuɗaɗen waje ta zahiri ta tashi daga dala biliyan 23 a ƙarshen shekarar 2024 zuwa dala biliyan 35 a ƙarshen shekarar 2025.

Rahoton ya ƙara da cewa Naira ta ƙara ƙarfi da kashi 10 cikin ɗari idan aka kwatanta da dalar Amurka a watan Maris na shekarar 2026, sakamakon ingancin yanayin kasuwa da kuma ƙarin shigowar kuɗaɗen waje.

IMF ya kuma yaba wa CBN saboda jajircewar sa wajen ci gaba da amfani da tsarin canjin kuɗi mai sassauci, yana mai cewa manufar ta inganta yadda kasuwa ke aiki tare da ƙara yawan kuɗaɗen da ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ke aikowa ta hanyoyin hukuma.

A ɓangaren bankuna kuwa, IMF ya bayyana shirin ƙarfafa jarin bankuna da ake gudanarwa a matsayin wani babban ci gaba da zai ƙarfafa tsarin kuɗi da kuma tallafa wa bunƙasar tattalin arziki na dogon lokaci.

Asusun ya lura cewa wannan shiri ya ƙara wa bankunan ƙasar ƙarfin jure matsin tattalin arziki tare da ba su damar tallafa wa ci gaban kamfanoni masu zaman kan su da bunƙasar tattalin arziki gaba ɗaya.

Sai dai IMF ya yi gargaɗin cewa har yanzu akwai wasu haɗurra a tsarin bankunan ƙasar, musamman ƙaruwar adadin kuɗaɗen da aka ranta, amma har yanzu ba a biya ba, da kuma yawan zuba jari a takardun bashin gwamnati.

Rahoton ya nuna cewa yawan kuɗaɗen rance da ba a biya ba ya kai kashi 8 cikin ɗari a zangon uku na shekarar 2025, wanda ya zarce matakin da ƙa’idojin banki suka amince da shi, sakamakon janye sassaucin dokokin da aka samar a lokacin annobar COVID-19.

Sai dai kuma duk da waɗannan haɗurran, IMF ya ce matsin lamba ga tsarin bankunan ƙasar ya ragu sosai idan aka kwatanta da halin da aka fuskanta tsakanin shekarun 2023 da 2024.

Rahoton ya kuma yi maraba da ƙoƙarin da CBN ke yi na daidaita tsarin bankunan Nijeriya da ƙa’idojin ‘Basel III’ ta hanyar ƙarfafa gwaje-gwajen juriyar bankuna, gyaran tsarin kula da kuɗin ruwa da kuma ƙarfafa matakan kariyar jarin bankuna.

IMF ya buƙaci hukumomi su hanzarta aiwatar da muhimman gyare-gyare kamar tsarin ƙarin kariyar jari a lokacin bunƙasar tattalin arziki da kuma ƙa’idar adadin kuɗin ruwa domin ƙara ƙarfafa tsarin kuɗi.

Asusun ya yaba da cire Nijeriya daga jerin ƙasashen da ake sa-ido kan su da Hukumar FATF ke yi.

FATF dai ya cire sunan Nijeriya a watan Oktoba 2025, lamarin da ke nuna hakan a matsayin wata babbar alama ta ingantaccen tsarin gaskiya a harkokin kuɗi da kuma ƙarfafa sa ido na hukumomi.

IMF ya jaddada cewa ci gaba da tsauraran manufofin kuɗi, gyare-gyaren fannin kuɗi da kuma daidaiton canjin kuɗi za su kasance muhimman abubuwa wajen ci gaba da ƙarfafa amincewar masu zuba jari da kuma cimma bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa da haɗa kowa da kowa.

Rahoton ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai bunƙasa da kashi 4.1 cikin ɗari a shekarar 2026, sakamakon ci gaban ɓangaren ayyuka, noma da kuma ƙaruwar ɓangaren man fetur.

Tags: CBNIMF
Previous Post

Rigakafi: Tinubu ya kafa kwamitin gaggawa kan Ebola, ya amince da kashe naira biliyan 10 don shirin ba da kariya

Next Post

Nau’o’in Kama Mutane Ba Bisa Ƙa’ida Ba Guda 5 a Nijeriya

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Nau’o’in Kama Mutane Ba Bisa Ƙa’ida Ba Guda 5 a Nijeriya

Nau’o’in Kama Mutane Ba Bisa Ƙa’ida Ba Guda 5 a Nijeriya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!