• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya umurci bankuna su riƙa bibiyar dalilin yadda kwastomomi ke tura kuɗaɗe daga asusun kuɗaɗen wajen su, ko su fuskanci tarar naira miliyan 100

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
June 8, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025
Bankin CBN

Bankin CBN

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umurci bankuna da su ci gaba da sa-ido tare da rubuta dalilin duk wata mu’amalar taransifa ko canja kuɗaɗen ƙasashen waje daga asusun da kowane kwastoman su ke ajiye kuɗaɗen waje.

Sannan kuma CBN na mai gargaɗin cewa rashin bin wannan umarni na iya jawo hukuncin tarar har naira miliyan 100 kan bankin da ya yi sakaci wajen ƙin bibiyar.

Wannan ƙarin haske ya biyo bayan matakin CBN na soke buƙatar masu asusun ajiyar kuɗaɗen waje na yau da kullum, tare da umarnin su cike ‘Form A’ kafin su tura kuɗaɗen ƙasashen waje daga asusun su.

A cikin ƙa’idojin da ke cikin bugu na huɗu na Kundin Dokokin Kasuwancin Musayar Kuɗaɗen Ƙasashen Waje, wanda a Turance ake kira ‘Foreign Exchange Manual’, CBN ya bayyana cewa masu asusun kuɗaɗen waje na yau da kullum suna da ’yancin amfani da kuɗaɗen da ke cikin asusun su domin halastattun mu’amaloli, ba tare da buƙatar ‘Form A ba’.

Sai dai kuma, bankin ya jaddada cewa dole ne bankuna su rubuta dalilin kowace mu’amala tare da sanya ta a madaidaicin rukuni a ƙarƙashin Kundin Lambobin Tsarin Gudanar da Musayar Kuɗaɗen Ƙasashen Waje, wato ‘Foreign Exchange Management System’ (FEMS Code Book).

Ana sa ran wannan mataki zai sauƙaƙa wa kwastomomi canja kuɗaɗen ƙasashen waje daga asusun su na ajiyar kuɗaɗen waje, tare da tabbatar da cewa masu sa-ido kan harkokin kuɗi za su ci gaba da bibiyar yadda kuɗaɗen ƙasashen waje ke gudana a cikin tsarin dokokin Nijeriya.

A ƙarƙashin waɗannan ƙa’idoji, masu asusun za su iya cire kuɗi ko biyan kuɗaɗe ta hanyar tsabar kuɗi, canjin kuɗi ta waya da sauran hanyoyin da aka amince da su.

Haka nan CBN ya kuma amince wa kwastomomi su yi amfani da tsabar kuɗin su na ƙasashen waje da ke cikin asusun su, har zuwa adadin dala 10,000 a rana, ko makamancin sa a wasu kuɗaɗen ƙasashen waje, domin yin canjin kuɗi ta waya, matuƙar bankuna sun gabatar da rahotannin da ke bayyana dalilin waɗannan mu’amaloli.

Babban bankin ya kuma bayyana cewa mutanen da ke buɗe ko sanya kuɗaɗe a asusun ajiyar kuɗaɗen wajen su, ba lallai ne su bayyana tushen kuɗaɗen ƙasashen wajen da suka ajiye ba. Duk da haka, dole ne dukkan mu’amalolin su kasance cikin bin dokokin yaƙi da halasta kuɗaɗen haram da kuma hana ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci.

Wannan sabon ƙarfafa matakin tattara bayanai wani ɓangare ne na ƙoƙarin CBN na ƙara ƙarfafa sa-ido kan kasuwar musayar kuɗaɗen ƙasashen waje ta Nijeriya tare da inganta bin doka da oda a tsakanin cibiyoyin kuɗi.

Bisa ga ƙa’idojin, duk wani bankin da aka ba izinin gudanar da harkokin musayar kuɗaɗen ƙasashen waje da ya aiwatar da wata mu’amala ba tare da cikakkun takardun shaida ba, zai iya fuskantar hukunci mai tsauri.

Kundin dokokin ya tanadi tarar naira miliyan 100 saboda gazawar samar da takardun da ake buƙata, baya ga tarar naira miliyan 10 kan kowace mu’amala da aka gano ta karya ƙa’idojin.

Masu fitar da kaya zuwa ƙasashen waje za su ci gaba da samun cikakkiyar damar amfani da kuɗaɗen da ke cikin asusun ajiyar kuɗaɗen wajen su, domin halattattun mu’amaloli. Sai dai idan aka canja kuɗaɗen zuwa wani mutum ko kamfani na uku, dole ne bankuna su tabbatar da cewa an rubuta dalilin mu’amalar yadda ya kamata tare da sanya ta ƙarƙashin lambar amfani da ta dace.

Masana harkokin kuɗi sun bayyana cewa wannan sabon umarni na nuna ƙoƙarin CBN wajen daidaita tsakanin sauƙaƙa samun damar amfani da kuɗaɗen ƙasashen waje da kuma tabbatar da gaskiya da bayyana gaskiya a kasuwar musayar kuɗi.

Tags: Babban Bankin Nijeriya (CBN)
Previous Post

Sabon Kundin Dokokin Canjin Kuɗi: Yadda CBN ke ƙoƙarin hana naira tambotsai a kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta Nijeriya 

Next Post

Amurka ta hana alƙalin wasa ɗan Somaliya Omar Aytan shiga ƙasar ta don halartar Gasar Kofin Duniya

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Amurka ta hana alƙalin wasa ɗan Somaliya Omar Aytan shiga ƙasar ta don halartar Gasar Kofin Duniya

Amurka ta hana alƙalin wasa ɗan Somaliya Omar Aytan shiga ƙasar ta don halartar Gasar Kofin Duniya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!