• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Zaɓen fidda gwanin APC ƙwarin gwiwar ɗorewar dimokiraɗiyya ne, inji Tinubu 

Wakilin Mu by Wakilin Mu
May 23, 2026
in Siyasa
A A
0
Zaɓen fidda gwanin APC ƙwarin gwiwar ɗorewar dimokiraɗiyya ne, inji Tinubu 
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen kaɗa ƙuri’a a zaɓen fidda gwani na APC da aka gudanar a mazaɓar Ikoyi-Obalende Ward L2 da ke Legas a ranar Asabar

Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen kaɗa ƙuri’a a zaɓen fidda gwani na APC da aka gudanar a mazaɓar Ikoyi-Obalende Ward L2 da ke Legas a ranar Asabar

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar a faɗin ƙasar nan a matsayin wata alama ta ƙarfi da bunƙasar dimokiraɗiyyar cikin gida a jam’iyyar mai mulki.

Tinubu ya bayyana haka ne bayan ya kaɗa ƙuri’ar sa a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a mazaɓar Ikoyi-Obalende Ward L2 da ke Jihar Legas a ranar Asabar.

Shugaban ya ce tsarin ya bai wa membobin jam’iyya a matakin ƙasa damar taka rawar gani wajen zaɓen shugabannin su, yana mai cewa hakan na ƙara ƙarfafa tsarin dimokiraɗiyya.

Ya ce: “Wannan wata alama ce ta dimokiraɗiyyar cikin gida, kuma an gudanar da ita yadda aka tsara. Siyasar tushe ce wadda ke bai wa kowane mamba damar shiga cikin tsarin zaɓe.”

Ya ƙara da cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana da tsari, lamarin da ya nuna cewa APC tana da ingantaccen tsarin gudanar da harkokin ta na cikin gida.

Tinubu ya yaba wa gwamnoni da shugabannin jam’iyyar a jihohi daban-daban kan yadda suka gudanar da matakan shirye-shiryen zaɓen, tun daga zaɓukan gundumomi zuwa tantance wakilai da rajistar mambobi.

A cewar sa, yadda aka gudanar da waɗannan matakai ya nuna cewa ana iya bai wa dimokiraɗiyya maki masu yawa a ƙasar nan.

Shugaban ya jaddada cewa APC za ta ci gaba da rungumar tsarin dimokiraɗiyya mai gaskiya da bai wa membobi damar zaɓar shugabannin su cikin ‘yanci, yana mai cewa hakan shi ne ginshiƙin cigaban siyasa mai ɗorewa.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu bayan ya kaɗa ƙuri’ar sa a zaɓe na fidda gwani yau a Legas

Ya kuma yaba wa jami’an zaɓe, shugabannin jam’iyya da hukumomin tsaro bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da zaman lafiya da gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.

Tinubu ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da mara wa cibiyoyin dimokiraɗiyya baya tare da ƙarfafa haɗin kai na ƙasa.

Har ila yau, ya sake tabbatar da kudirin gwamnatin sa na ci gaba da bin tafarkin dimokiraɗiyya, inganta shugabanci da aiwatar da manufofin da za su inganta rayuwar al’ummar Nijeriya tare da tabbatar da zaman lafiyar siyasa a ƙasar nan.

Previous Post

Hausa da Hausawa a Ghana

Next Post

Related Posts

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko
Siyasa

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu
Siyasa

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

September 10, 2026
Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027
Siyasa

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

September 9, 2026
Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2
Siyasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2

September 2, 2026
Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20
Siyasa

Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20

August 26, 2026
Siyasa

Tinubu ya janye jerin sunayen Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC – Rahoto

August 25, 2026
Next Post

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!