• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Taron Kwamitin Manufofin Kuɗi na 305: Masana da masu ƙananan sana’o’i sun yaba da barin kuɗin ruwa da CBN ya yi a kashi 26.5%

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
May 22, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Cikar wa’adin ƙarfafa jari: Yadda bankunan Nijeriya suka bazama tara Naira tiriliyan 4.6 a ƙoƙarin cika sharuɗɗan CBN
Hedikwatar CBN a Abuja

Hedikwatar CBN a Abuja

Masana tattalin arziki, manazarta harkokin kuɗi da kuma masu ƙananan sana’o’i sun yaba da matakin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ɗauka na barin kuɗin ruwa na Manufofin Kuɗi (MPR) a matakin kashi 26.5%.

Waɗanda aka sanya da su domin jin ra’ayin su dangane da adadin kuɗin ladar karɓar lamiɗo a bankuna, wato kashi 26.5%, sun bayyana matakin a matsayin mai taka-tsantsan, amma kuma na wajibi domin kare daidaiton tattalin arziki a daidai lokacin da hauhawar farashi ke ci gaba da zama barazana.

An bayyana wannan matsayar ne bayan taro na 305 na Kwamitin Manufofin Kuɗi (MPC), inda CBN ya bar dukkan manyan manufofin kuɗi a yadda suke ba tare da wani canji ba na ƙari ko ragin adadi ba.

Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa wannan mataki na nuna ƙoƙarin CBN domin daidaita tsakanin yaƙi da hauhawar farashi da kuma kauce wa ƙara wa ‘yan kasuwa matsin lamba, musamman ma waɗanda ke fama da tsadar rance, rashin daidaiton canjin kuɗi, tashin farashin makamashi da kuma raunin buƙatar masu saye.

Masana tattalin arziki da suka zanta da Nairametrics sun ce matakin na barin kuɗin ruwa yadda yake na nuna sabon salon taka-tsantsan a manufofin kuɗi na CBN, musamman bayan tsauraran matakan da aka ɗauka na dogon lokaci domin daidaita farashi da kasuwar canjin kuɗi.

Da dama daga cikin masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa ci gaba da riƙe wannan ƙimar kuɗin ruwa zai bai wa ‘yan kasuwa da masu zuba jari sauƙi kaɗan, bayan fama da tsadar kuɗin gudanar da harkoki a cikin shekarar da ta gabata.

“Barin kuɗin ruwa yadda yake na aika saƙon taka-tsantsan da kwanciyar hankali. ‘Yan kasuwa da masu zuba jari sun sha wahala sosai saboda tsauraran matakan da aka ɗauka a bara. Wannan mataki zai bai wa tattalin arziki damar samun sauƙin karsashi da yin hoɓɓasa,” inji masanin tattalin arziki, Dakta Albert Miyaki.

Ya ƙara da cewa, “Kuɗin ruwa har yanzu yana da tsada sosai ga ‘yan kasuwa. Duk da cewa yaƙi da hauhawar farashi yana da muhimmanci, akwai kuma buƙatar tallafa wa samar da kayayyaki da ƙirƙirar ayyukan yi.”

Babban Daraktan Cibiyar Bunƙasa Kamfanoni Masu Zaman Kansu Kamfanoni (CPPE), Dakta Muda Yusuf, ya ce ƙungiyar “na maraba da matakin da CBN ya ɗauka na ci gaba da riƙe dukkan muhimman manufofin kuɗi a taro na 305 na Kwamitin Manufofin Kuɗi.”

Yusuf ya ƙara da cewa matakin na nuna “fahimta mai amfani, mai taka-tsantsan kuma mai zurfi kan matsalolin hauhawar farashi da tattalin arzikin Nijeriya ke fuskanta a yanzu.”

CPPE ta kuma yaba wa CBN bisa abin da ta kira kyakkyawan tafiyar da manufofin kuɗi da kuma ɗan daidaiton da aka samu a kasuwar canjin kuɗi a ‘yan watannin nan.

Masu ƙanana da matsakaitan sana’o’i a Nijeriya (SMEs) sun ce matakin na kauce wa sake ƙara kuɗin ruwa zai taimaka wajen rage matsin lamba da suke ciki.

Da dama daga cikin SMEs sun koka da tsadar rance, inda kuɗin ruwa daga bankunan kasuwanci ya haura kashi 30% a lokuta da dama can baya.

Wata ‘yar kasuwa daga Abuja, Misis Chioma Nwosu, ta ce kamfanoni da dama na fama da rashin samun rance mai sauƙi da suke buƙata domin faɗaɗa harkokin su da kuma ci gaba da gudanar da ayyukan su.

“Yawancin SMEs ba za su iya rayuwa da kuɗin ruwa sama da kashi 30% ba.

A baya, kamfanoni da dama sun fara rage ma’aikata saboda sun kasa samun kuɗin sayen kaya, kayan aiki ko kuma faɗaɗa sana’a. Aƙalla, rashin ƙara kuɗin ruwa a wannan karo ya kawo ɗan sauƙi,” inji ta.

Wani masanin harkokin zuba jari, Tunde Adeyemi, ya ce matakin MPC na iya ƙara wa masu zuba jari ƙwarin gwiwa tare da tallafa wa harkokin kasuwar hannayen jari saboda samar da tabbacin manufofi.

A fahimtar sa, “Yan kasuwa sun damu da ci gaba da tsaurara manufofin kuɗi. Barin kuɗin ruwa yadda yake zai kawo tabbaci kuma zai iya jawo hankalin masu zuba jari da ke jiran ganin yadda abubuwa za su kaya.”

Sai dai masana sun jaddada cewa yanayin kuɗin ruwa a yanzu har yanzu yana da tsauri ga fannoni masu samar da kayayyaki kamar masana’antu, noma da ƙananan sana’o’i waɗanda suka dogara sosai kan samun rance mai sauƙi.

Masu ruwa da tsaki sun ce matakin na iya taimakawa wajen daidaita tunanin masu zuba jari da kuma kiyaye amincewa da tsarin manufofin kuɗi na Nijeriya a daidai lokacin da hauhawar farashi, matsin canjin kuɗi da kuma matsalolin siyasar duniya ke ci gaba da haifar da rashin tabbas ga tattalin arzikin ƙasashe masu tasowa.

SMEs sun kuma bayyana cewa matsalolin tsaro, rashin ingantattun hanyoyi da ababen more rayuwa, matsalolin sufuri da kuma tsadar makamashi na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa hauhawar farashi.

Ra’ayin gama gari tsakanin masu ruwa da tsaki shi ne, duk da cewa dakatar da ƙara kuɗin ruwa a yanzu abu ne mai kyau, akwai yiwuwar a buƙaci rage kuɗin ruwa a hankali idan hauhawar farashi ya ci gaba da sauka.

CBN ya bar MPR a matakin kashi 26.5% ne bayan rage shi da maki 50 daga kashi 27% a taron MPC da ya gabata da aka gudanar a watan Fabrairun 2026.

Kwamitin ya kuma bar sauran muhimman manufofin kuɗi yadda suke.

Da ma tun tsawon mako ɗaya kafin zuwan ranar taron, sai da masana kasuwannin kuɗi suka yi hasashen cewa MPC zai bar kuɗin ruwa yadda yake, saboda matsin hauhawar farashi da rashin tabbas a tattalin arzikin duniya.

CBN ya ci gaba da bin salon taka-tsantsan a manufofin kuɗi domin yaƙi da hauhawar farashi da kuma daidaita darajar naira.

Previous Post

Albarkacin manufofin CBN, Nijeriya ta samu jinjina da ƙarin daraja daga S&P

Next Post

Hausa da Hausawa a Ghana

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Hausa da Hausawa a Ghana

Hausa da Hausawa a Ghana

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!