• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Abba Yusuf ya tura wa majalisa sunan Garo ta tantance shi don zama Mataimakin Gwamna

ALI KANO by ALI KANO
April 22, 2026
in Siyasa
A A
0
Abba Yusuf ya tura wa majalisa sunan Garo ta tantance shi don zama Mataimakin Gwamna
Alhaji Murtala Sule Garo

Alhaji Murtala Sule Garo

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya aika da sunan Alhaji Murtala Sule Garo zuwa Majalisar Dokokin Jihar domin tantancewa da tabbatar da shi a matsayin Mataimakin Gwamna.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, Mustapha Muhammad, ya sanya wa hannu.

Naɗin ya yi daidai da Sashe na 191(3) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima), wanda ya bai wa gwamna ikon naɗa mataimakin gwamna idan gurbi ya samu.

Matsayin ya zama babu kowa a ciki ne bayan murabus na ƙashin kan sa da tsohon Mataimakin Gwamna, Kwamared Abdussalam Gwarzo, ya yi a ranar 27 ga Maris.

Bayan tattaunawa sosai da ya yi da masu ruwa da tsaki, gwamnan ya buƙaci Majalisar ta ba da amincewar da ake buƙata domin tabbatar da naɗin Garo.

Garo, wanda ɗan shekara 48 ne, gogaggen ɗan siyasa ne wanda ya kwashe sama da shekaru ashirin yana harkar siyasa inda ya riƙe muƙami da aka zaɓe shi ko na naɗi.

Ya taɓa zama Sakataren Tsare-tsare na Jiha na jam’iyyar sa, Mai Bai wa Gwamnan Jihar Kano Shawara ta Musamman, sannan aka zaɓe shi Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo.

Haka kuma ya taɓa zama Shugaban ƙungiyar ALGON ta Kano, Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, sannan ya kasance ɗan takarar Mataimakin Gwamna na jam’iyyar APC a babban zaɓen 2023.

Tags: Abba Kabir YusufKanoMajalisar DokokiMataimakin GwamnaMurtala Sule Garo
Previous Post

Tinubu ya naɗa Fatima Zuntu shugabar hukumar NBMA

Next Post

Minista ya lissafa nasarorin gwamnatin Tinubu ga ‘yan jarida na duniya

Related Posts

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko
Siyasa

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu
Siyasa

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

September 10, 2026
Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027
Siyasa

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

September 9, 2026
Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2
Siyasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2

September 2, 2026
Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20
Siyasa

Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20

August 26, 2026
Siyasa

Tinubu ya janye jerin sunayen Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC – Rahoto

August 25, 2026
Next Post
Minista ya lissafa nasarorin gwamnatin Tinubu ga ‘yan jarida na duniya

Minista ya lissafa nasarorin gwamnatin Tinubu ga 'yan jarida na duniya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!