• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gargaɗi, sharuɗɗa da wa’adin da CBN ya gindaya kan BVN don tsaurara matakan tsare kuɗaɗen kwastomomi a bankuna

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
April 27, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Gargaɗi, sharuɗɗa da wa’adin da CBN ya gindaya kan BVN don tsaurara matakan tsare kuɗaɗen kwastomomi a bankuna
Kwastomomi a banki

Kwastomomi a banki

Matakin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ɗauka na nufin rage zamba, ƙarfafa kariyar bayanan mutum, da kuma kare tsarin kuɗi na Nijeriya.

Yayin da CBN ke shirin fara aiwatar da sabbin dokokin ‘Bank Verification Number’ (BVN) daga ranar 1 ga Mayu, 2026, akwai muhimman ƙa’idoji da kowane mai asusun banki ya kamata ya sani kafin wa’adin ya cika.

Sabon tsarin ya kawo tsauraran dokoki kan canjin lambar waya, amfani da na’ura, da iyakar adadin ma’amaloli.

Matakin na nufin rage zamba, ƙarfafa kariyar shaidar mutum, da kuma kare tsarin kuɗi a ƙasa.

Manhajar Banki ta Wayar Salula (Mobile Banking App):

Daga yanzu, za a taƙaita amfani da manhajar banki a kan waya guda ɗaya kawai a lokaci guda.

Idan ka shiga manhajar bankin ka a wata sabuwar waya, tsohuwar na’urar za ta daina aiki nan take, sannan a buƙaci ƙarin matakan tabbatar da kai.

Ƙarfafa Sa-ido kan Zamba:

An umurci bankuna su sanya duk wata lambar BVN da aka danganta da ayyukan da ake zargi na zamba cikin jerin lambobin da ake sa-ido kan su na awanni 24. A wannan lokacin, ana iya taƙaitawa ko kulle asusun da abin ya shafa, yayin da banki zai tuntuɓi mai asusun don tabbatarwa.

Canjin Lambar Waya:

A ƙarƙashin sabuwar doka za a iya canza lambar wayar da ke da alaƙa da BVN sau ɗaya kacal a rayuwa.

Wannan mataki na nufin daƙile yawaitar zambar sauya kati wato ‘SIM-swap’, inda masu laifi ke karɓe lambar waya domin samun damar shiga asusun banki.

Saboda haka ana bada shawara ga kwastomomi su haɗa BVN ɗin su da lambar waya mai ƙarfin tsaro kuma ta dindindin — musamman wadda ke da alaƙa da lambar shaidar ɗan ƙasa ta NIN (National Identification Number).

Mafi Karancin Shekarun Yin Rijistar BVN:

CBN ya gindaya shekaru 18 a matsayin mafi ƙarancin shekaru don yin rijistar BVN.

Wannan yana nufin yara ƙanana ba za su iya mallakar BVN da kan su ba. Maimakon haka, iyaye ko masu kula za su yi amfani da tsare-tsaren banki na yara domin sarrafa kuɗaɗen su.

Adadin Yawan Ma’amala Da Banki:

Duk wanda ya kunna manhajar banki a sabuwar waya zai fuskanci adadin iyakar ma’amala ta ₦20,000 cikin awanni 24 na farko.

Wannan mataki kariya ce domin rage asara idan aka samu matsala yayin saita wayar.

Abin da Ya Kamata Ka Yi Kafin 1 ga Mayu, 2026:

Ana ƙara jaddada wa kwastomomi su ɗauki matakan kariya domin guje wa tangarɗa.

Tabbatar da lambar wayar da ke haɗe da BVN ɗin ka: Ta kasance mai aiki, mai tsaro, kuma taka ce dindindin.

Sabunta bayanai da wuri: Idan kana buƙatar canza lambar waya, yi hakan kafin wa’adin ya cika.

Tsauraran matakan shiga (login):

Musamman idan kana sauya waya ko sake girka manhajar banki.

A ƙarƙashin sabuwar doka, dole ne cibiyoyin kuɗi su kafa kuma su kula da sa-ido na wucin gadi ga BVN da ake zargi da alaƙa da ma’amaloli masu hatsari a cikin tsarin banki.

Tags: Babban Bankin NijeriyabankiBVNCBNkwastomomi
Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta fara aikin samar da lantarki ta hasken rana na naira biliyan 3.8 a Jami’ar ADUSTECH da ke Kano

Next Post

Rikicin shugabanci a ADC: Ɓangaren David Mark ya rubuta wa CJN takarda, ya roƙi a gaggauta yanke hukunci

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Rikicin shugabanci a ADC: Ɓangaren David Mark ya rubuta wa CJN takarda, ya roƙi a gaggauta yanke hukunci

Rikicin shugabanci a ADC: Ɓangaren David Mark ya rubuta wa CJN takarda, ya roƙi a gaggauta yanke hukunci

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!