Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Dakta Muttaqha Rabe Darma a matsayin sabon Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane na Tarayya a yau Juma’a.
Rantsar da Darma, wanda ɗan asalin Jihar Katsina ne, ya biyo bayan amincewa da takardar naɗin sa da Majalisar Dattawa ta yi. Ya maye gurbin Ahmed Musa Ɗangiwa wanda ya yi murabus kwanan nan.
A wani taƙaitaccen biki da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa, Tinubu ya taya sabon ministan murna, inda ya bayyana cewa ya zo ne a daidai lokacin da ƙasar nan ke fuskantar ƙalubalen neman cigaba.
Shugaban ya yaba wa Darma inda ya ce: “Kuna da ƙwarewa da kyakkyawan tarihin aiki. A matsayin mu na shugabanni, muna buƙatar ƙwararru irin ku. Babu shakka kun taka rawar gani a duk inda kuka yi aiki a baya, don haka kun dace da wannan matsayi.”

Wanene Dakta Muttaqha Darma?
Dakta Darma babban masani ne kuma ƙwararren mai gudanarwa wanda ya yi karatun digiri na uku a fannin harkar kasuwanci daga Jami’ar Liverpool, da kuma wani digiri na ukun a fannin “Industrial Engineering” daga Amurka.
Tarihin sa na karatu da aiki ya hada da:
• Digiri na farko a fannin “Mechanical Engineering” daga Jami’ar Bayero ta Kano (BUK).
• Ya taɓa zama Sakataren Gudanarwa na Asusun Tallafa wa Fasahar Man Fetur (PTDF) daga 2008 zuwa 2012.
• Ya riƙe muƙaman Kwamishinan Ayyuka da Gidaje, da kuma Kwamishinan Matasa da Walwalar Jama’a a Jihar Katsina.
• Ya taɓa zama malami a Jami’ar Bayero ta Kano.
Kafin wannan naɗe-naɗen, Darma shi ne Shugaban Cibiyar Bunƙasa Ɗan’adam ta Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina.
Sabon ministan ya sha alwashin yin amfani da ƙwarewar sa domin tabbatar da cewa an samar wa ‘yan Nijeriya gidaje masu rahusa da kuma inganta biranen ƙasar nan kamar yadda tsarin gwamnati mai ci ya tanada.







