Mai Martaba Sarkin Kano, Dakta Muhammadu Sanusi II, ya nuna damuwa kan yadda Gwamnatin Tarayya take ci gaba da dogaro da karɓar bashi duk da cire tallafin man fetur da ta yi, inda ya yi tambaya kan alƙiblar da harkokin kuɗin ƙasar nan suke fuskanta da ɗorewar su.
Sanusi, wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) ne, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka watsa a gidan talbijin na News Central TV a yau Juma’a, inda ya yi nazari mai zurfi kan halin da harkokin kuɗin Nijeriya suke ciki a yanzu.
Duk da yake ya amince cewa cire tallafin mai da sassauta tsarin canjin kuɗaɗen waje gyare-gyare ne da suka zama dole, ya yi gargaɗin cewa rashin dacewar lokacin aiwatar da su da kuma rashin tsauraran matakan kula da harkokin kuɗi na iya lalata fa’idojin da ake tsammani.
A cewar sa, dogon tarihin da Nijeriya ke da shi na tallafa wa matatun mai na ƙasashen waje tare da yin watsi da ƙarfin tace mai na cikin gida yana nuna wata matsala ce ta tsarin da ya kamata a gyara.
Sarkin ya ce: “Tun da daɗewa nake cewa tsarin tallafin mai ba mai ɗorewa ba ne. Ba za mu ci gaba da tallafa wa matatun mai na ƙasashen waje ba. Mu ƙasa ce mai samar da mai. Ba zai yiwu mu riƙa raya matatun waje alhali namu ba sa aiki ba.”
Sai dai ya nuna kyakkyawan fata kan sababbin cigaban da aka samu a fannin, yana mai cewa an fara karkata zuwa tace mai a cikin gida tare da rage dogaro da shigo da man fetur daga waje.
Ya ce: “A yau muna da yanayin da muke da matatar mai tamu a cikin gida. Ba ma shigo da kayan man fetur. Har ma muna fitarwa zuwa Turai, kuma wannan abu ne mai kyau ga tattalin arziki.”
Duk da goyon bayan da yake bai wa gyare-gyaren, Sanusi ya nuna damuwa kan yadda aka tsara su da kuma lokacin da aka aiwatar da su, yana mai cewa akwai wasu muhimman matakai da wataƙila an yi watsi da su.
“Tsarin canjin kuɗi na bogi, musamman idan ana buga kuɗi, ba zai yi aiki ba. Dole ne a samu faɗuwar darajar kuɗi,” inji shi.
“Ni a gani na, cire tallafi ko sassauta canjin kuɗi abubuwa ne masu kyau. Amma shin an yi su a daidai lokacin da ya dace? Wannan tambaya ce. Shin akwai wasu abubuwan da ya kamata a yi amma ba a yi su ba? Waɗannan ma wasu batutuwa ne.”
Ya ce aiwatar da sassauta canjin kuɗi a yanayin da tsarin kuɗi yake da sassauci ya taimaka wajen faɗuwar darajar naira sosai.
“Ba ya isa a ce an cire tallafi kawai. Dole ne a cire shi. Idan ka kai matsayin da kaso 100 na kuɗaɗen shiga naka ke tafiya wajen biyan bashin da aka ci, ba za ka iya ci gaba a haka ba. To daga ina kuɗin za su fito?
“Amma idan ka cire tallafi kuma ka sassauta canjin kuɗi a yanayin da babu tsauraran matakan kula da yawan kuɗi, kafin ka daidaita yawan kuɗin da ke yawo, naira za ta faɗi ƙasa warwas. Wannan matsalar lokaci ce.”
Sanusi ya kuma tambayi dalilin da ya sa gwamnati take ci gaba da karɓar bashi mai yawa bayan cire biyan tallafi.
Ya ƙara da cewa: “Mun cire tallafi. Yanzu muna amfani da kuɗin. Abin da bai kamata mu gani ba shi ne rashin daidaita harkokin kuɗi. Ba za ka rage almubazzaranci sannan ka ci gaba da karɓar bashi ba. Na faɗi haka tun da farko. Ya kamata a ga amfanin hakan.
“Idan ba ka biyan tallafi kuma kana da kuɗin, me ya sa har yanzu muke ci gaba da karɓar bashi? Don me ake karɓar bashin?”
Sababbin alƙaluma sun ƙara tabbatar da damuwar sa. Rahotanni a watan Afrilu sun nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta ƙara shirin karɓar bashin shekarar 2026 da tiriliyan ₦11.31, wanda ya kai jimillar bashin da ake sa ran za a karɓa zuwa tiriliyan ₦29.20.
A wani labarin mai alaƙa da wannan, yanzu haka Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dattawa kan sabon bashin dala miliyan 516 da yake nema domin tallafa wa aikin babbar hanyar Sakkwato zuwa Badagiri.







