• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Gwamnan Bauchi zai bayyana sauya sheƙar sa zuwa ADC ranar Alhamis

* Mun so shiga APC aka ƙi karɓar mu, inji shi

Fati Abdul by Fati Abdul
April 1, 2026
in Siyasa
A A
0
Gwamnan Bauchi zai bayyana sauya sheƙar sa zuwa ADC ranar Alhamis
Gwamna Bala Mohammed (na 2 daga dama) tare da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Babachir Lawal (na 2 daga hagu) lokacin ziyarar a Fadar Gwamnatin Jihar Bauchi, a Bauchi yau Talata

Gwamna Bala Mohammed (na 2 daga dama) tare da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Babachir Lawal (na 2 daga hagu) lokacin ziyarar a Fadar Gwamnatin Jihar Bauchi, a Bauchi yau Talata

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed (Ƙaura), ya nuna yiwuwar ficewar sa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), inda ya bayyana African Democratic Congress (ADC) a matsayin dandalin siyasar da ya fi so, sakamakon tsananin rikicin cikin gida da ke ƙara ƙamari a cikin jam’iyyar su ta adawa.

Gwamnan, wanda kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP, ya bayyana hakan ne a yau Talata yayin da yake karɓar wata babbar tawaga ta ADC a Fadar Gwamnati da ke Bauchi.

Tawagar tana ƙarƙashin jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Babachir Lawal, waɗanda suka je bisa umurnin shugabannin jam’iyyar na ƙasa.

Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan ganawar sirri da suka yi, Bala Mohammed ya koka kan yadda rarrabuwar kai take ƙara tsananta a cikin PDP, yana mai bayyana cewa ƙoƙarin sasanta ɓangarorin da ke rikicin ya ci tura.

Ya ce: “Mun tsinci kan mu a cikin wani yanayi mai matuƙar tsanani. Na yi duk mai yiwuwa domin ganin an samu sulhu, amma hakan bai yi nasara ba.”

Gwamnan ya ƙara da cewa an kafa kwamitoci a matakin ƙasa da jiha domin nemo mafita, ciki har da tuntubar wasu jam’iyyun siyasa.

Sai dai ya ce har ma yunƙurin tuntuɓar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulkin ƙasa bai haifar da ɗa mai ido ba.

Ya bayyana ƙoƙarin da ya yi na shiga APC amma aka ƙi karɓar sa, ya ce, “Mun gwada shiga dukkan jam’iyyu, har da APC, amma abin takaici mun gano cewa ba a son mu a can.”

A wannan yanayi, Bala ya ce ADC ita ce ta fi nuna maraba da shi kuma ta zama zaɓin da ya fi dacewa da shi a halin yanzu.

“A yanzu, ADC na bayyana a matsayin dandalin da ke karɓar mu kuma mafi dacewa. Duk da haka, ba mu kammala tattaunawa ba. Muna ci gaba da tuntuɓar masu ruwa da tsaki domin kauce wa yin kuskure.”

Gwamnan ya nuna cewa tuntuɓa ta ƙarshe na ci gaba kuma sun kusa kammalawa, inda ake sa ran yanke hukunci nan ba da jimawa ba.

Ya ce: “Muna sane da muhimmancin lokaci. Za a kammala komai kafin ranar Alhamis domin mu ci gaba tare. Za ku ji cikakken matsayar mu.”

Bala ya kuma zargi cewa rikicin da ke addabar PDP yana ƙara tsananta ne sakamakon tsoma baki sa wasu ke yi daga waje, musamman yana zargin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da zama kanwa-uwar-gami a rikicin.

A cewar sa, irin waɗannan tasiri sun sa ƙoƙarin sulhu ya ƙara wahala tare da zurfafa rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar.

Ya kuma bayyana cewa ya yi ganawar musamman da manyan ‘yan siyasa, ciki har da shugabannin APC da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, domin warware matsalar, amma hakan bai samar da mafita mai ɗorewa ba.

Tun da farko, Babachir Lawal ya ce ziyarar tawagar ADC ɗin wani ɓangare ne na dabarun haɗa kan jam’iyyun adawa gabanin zaɓen shekarar 2027.

Ya bayyana cewa wannan yunƙuri ya samo asali ne daga shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, domin ƙarfafa ADC a matsayin ingantaccen zaɓin dandalin siyasa.

Ya ce: “Ceton Nijeriya a 2027 yana buƙatar haɗin kan dukkan ‘yan Nijeriya masu kishin ƙasa. Mun zo ne domin tattaunawa da Gwamna Bala Mohammed saboda ƙwarewar sa da gogewar sa a siyasa.”

Ya bayyana fatan cewa tattaunawar da ake yi za ta haifar da sakamako mai kyau, yana mai cewa a shirye ADC take ta karɓi gwamnan da magoya bayan sa.

Tags: ADCAPCBabachir LawalBala MohammedBauchiPDPsauya sheƙazaben2027
Previous Post

Nijeriya ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba – Gwamnatin Tarayya

Next Post

Gwamnatin Tarayya, ta Kano da Gidauniyar Ɗangote za su farfaɗo da Cibiyar Koyon Sana’o’i ta Ɗangote

Related Posts

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko
Siyasa

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu
Siyasa

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

September 10, 2026
Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027
Siyasa

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

September 9, 2026
Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2
Siyasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2

September 2, 2026
Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20
Siyasa

Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20

August 26, 2026
Siyasa

Tinubu ya janye jerin sunayen Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC – Rahoto

August 25, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya, ta Kano da Gidauniyar Ɗangote za su farfaɗo da Cibiyar Koyon Sana’o’i ta Ɗangote

Gwamnatin Tarayya, ta Kano da Gidauniyar Ɗangote za su farfaɗo da Cibiyar Koyon Sana'o'i ta Ɗangote

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!