Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kano tare da Gidauniyar Ɗangote sun cimma yarjejeniyar haɓakawa, tare da kula da Cibiyar Koyon Sana’o’i ta Ɗangote (Dangote Ultramodern Skills Acquisition Centre) da ke Kano.
Bayanin wannan mataki yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Hukumar Ilimin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (STSB), Farfesa Ɗahiru Sale Mohammed, ya fitar a madadin Kwamishinan Ilimi na jihar.
A ƙarƙashin wannan sabuwar dangantaka, ɓangarorin uku za su ɗauki nauyin garambawul da inganta kayan aikin cibiyar, sannan su tabbatar da ɗorewar ayyukan ta na tsawon shekaru 20 masu zuwa.
Cibiyar, wadda aka gina domin bai wa matasa horo kan ƙwarewar hannu da fasahar zamani, ana sa ran za ta kasance ƙashin baya wajen rage raɗaɗin rashin aikin yi a jihar da ma maƙwabtan ta.
Farfesa Ɗahiru Sale ya bayyana cewa wannan yunƙuri zai tabbatar da cewa cibiyar ba ta durƙushe ba kamar yadda wasu ayyukan ke yi idan aka samu canjin gwamnati, duba da tsarin kula da ita na dogon lokaci da aka ƙulla.
Jihar Kano dai ita ce jiha mafi yawan jama’a a arewacin Nijeriya, inda matasa ke da kaso mafi tsoka.
Wannan cibiya za ta mayar da hankali ne wajen koyar da sana’o’in da suka dace da buƙatun ƙarni na 21, domin bai wa matasa damar dogaro da kan su maimakon jiran aikin gwamnati.
Sanarwar ta jaddada cewa an kammala dukkan shirye-shiryen fara aikin fito da sabuwar fuskar cibiyar nan ba da jimawa ba.







