• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Shettima ya karɓi gwamnan Adamawa cikin APC, ya ce jam’iyyar ta nuna siyasar cigaba a ƙarƙashin Tinubu

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
March 23, 2026
in Siyasa
A A
0
Shettima ya karɓi gwamnan Adamawa cikin APC, ya ce jam’iyyar ta nuna siyasar cigaba a ƙarƙashin Tinubu
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nantawe Yilwatda, ya bai wa Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, tutar jam’iyyar a matsayin alamar karɓar sa cikin jam’iyyar, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, yake kallo… a Yola yau.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nantawe Yilwatda, ya bai wa Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, tutar jam’iyyar a matsayin alamar karɓar sa cikin jam’iyyar, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, yake kallo… a Yola yau.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya tabbatar wa da Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, da magoya bayan sa cewa ba su shiga jam’iyyar APC a matsayin baƙi ba, sai dai a matsayin abokan hulɗa a wata manufa ta bai-ɗaya domin gina Nijeriya.

Ya ce shigar gwamnan cikin jam’iyyar mai mulki wata tunatarwa ce cewa dimokiraɗiyya na iya ɗorewa ne ba kawai ta hanyar sahihin zaɓin jama’a ba, har ma ta hanyar alhakin shugabannin siyasa wajen yin zaɓin da ke ƙarfafa tsarin da suke yi wa hidima.

Shettima ya faɗi haka ne yau a Yola, babban birnin Jihar Adamawa, lokacin da ya karɓi Gwamna Fintiri da magoya bayan sa cikin APC a madadin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Da yake jawabi ga taron jama’a mai ɗimbin yawa a Dandalin Mahmud Ribadu, wurin bikin, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya shaida wa sababbin ‘yan jam’iyyar cewa zuwan su yana nuna haɗuwa da wata manufa da ke sanya ‘yan Nijeriya a tsakiyar shugabanci, tare da fahimtar cewa iko ba manufa ba ne, illa nauyi ne.

Ya ce: “A madadin Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ina miƙa maku maraba ta gaskiya, Gwamna Fintiri, da dukkan magoya bayan ka da suka zo wannan tafiya a yau.

“Ku ba baƙi ba ne a wannan gida. Ku abokan hulɗa ne a wata manufa ta bai-ɗaya—gina ƙasa mai aiki, dimokiraɗiyya mai amfani, da makoma da ke cika burin al’ummar mu.”

Shettima ya bayyana dimokiraɗiyya a matsayin kasuwar zaɓi, “inda ake gwada ra’ayoyi, ake auna imani, kuma inda muradin jama’a ke samun bayyana,” yana mai cewa a ƙarƙashin Tinubu, APC ta nuna shugabanci na cigaba.

Shettima yana gabatar da jawabi a taron a Yola a yau

“Saboda haka ina farin cikin kasancewa tare da ku a wannan goyon baya ga siyasar cigaba da APC ta nuna ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu,” inji shi, ya ƙara da cewa jam’iyyar ta zama abar amincewa ga ‘yan Nijeriya.

Ya lura da cewa yawan sauya sheƙa daga sauran jam’iyyun siyasa zuwa APC yana nuna cewa “idan aka ba mutane zaɓi, za su fi karkata ga tsari, hangen nesa, da oda, da kuma jam’iyyar da ta fahimci nauyin shugabanci.”

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce jam’iyyar tana buƙatar hikima da sababbin tunani daga waɗanda suka daɗe a aikin gwamnati domin ta dace da buƙatun yau da gobe, yana mai cewa shigar Fintiri wata sabuwar gudunmawa ce ga jam’iyyar.

“Jam’iyyun siyasa, kamar ƙasashe, dole su sabunta kan su. Dole su daidaita. Dole su samo ƙarfi daga bambancin tunani domin su ɗore. Wannan haɗuwa ba ƙarshen abu ba ne; sabuntawar manufa ce, sabuntawar fata,” inji shi.

Manyan baƙi a taron a Dandalin Mahmud Ribadu a Yola

Shettima ya yaba da yadda Fintiri ke jagorantar Adamawa, yana mai cewa hanyoyi, ayyukan more rayuwa da sauran alamun cigaba a Yola na nuna ƙwazo da jajircewar sa.

“Waɗannan suna nuna shugabanci da ke fahimtar cewa auna gwamnati da sakamako ake yi. Saboda haka muna yabawa da ƙoƙarin ka, kuma muna sa ran haɗin gwiwa domin cigaban Adamawa da ƙasa baki ɗaya,” ya ƙara da cewa.

Sai dai ya tunatar da ‘yan jam’iyyar cewa aikin gina wata jam’iyya da za ta kasance zaɓin farko ga ‘yan Nijeriya ya fi komai wahala.

Tun da fari, sai da Shugaban APC na Ƙasa, Farfesa Nantawe Yilwatda, ya yaba da ayyukan raya ababen more rayuwa da Fintiri ya yi a Adamawa, yana mai cewa bai ga irin sa a wasu wurare ba, musamman hanyoyi.

“Mai Girma, ina alfahari da kai. Kana da kyau fiye da zama a jam’iyyar adawa. Kana da cancantar kasancewa cikin masu ci gaba. Barka da zuwa inda ya dace da kai,” inji shi.

Ya kuma yaba da nasarorin gwamnan a ɓangaren ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman fannoni.

A nasa ɓangaren, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya yaba da matakin da Fintiri ya ɗauka, yana mai cewa hakan zai ba shi damar haɗin gwiwa da sauran gwamnoni.

Haka zalika, Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC (PGF), Gwamna Hope Uzodimma na Jihar Imo, ya ce APC ita ce jam’iyyar da ta zo da Ajandar Sabuwar Fata ta Shugaba Tinubu domin sauya Nijeriya.

Ya ce shigowar Fintiri cikin APC zai kawo ƙarin cigaba ga jihar.

A nasa jawabin, Fintiri ya ce ya shiga APC ne domin haɗuwa da manufofi da shirye-shiryen Shugaba Tinubu da ke tafiya daidai.

“Shugaban Ƙasa ya yi abubuwa da dama, ya kuma sanya ƙasar nan a hanyar farfaɗowa, musamman a ɓangaren tattalin arziki. Mun zo domin mu ba shi da APC goyon baya domin samun nasara a zaɓen 2027,” inji shi.

Gwamnan ya ce zai tabbatar da nasarar APC a 2027, yana mai jaddada cewa, “Kudu ce ya kamata ta kammala wa’adin shekaru takwas.”

Babban abin da ya fi ɗaukar hankali a taron shi ne miƙa tutar APC ga Gwamna Fintiri a matsayin jagoran jam’iyyar a Adamawa.

Bayan haka, Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ya kai ziyarar girmamawa ga Lamiɗon Adamawa kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta jihar, Dakta Muhammadu Barkindo Aliyu Musɗafa.

Ya jaddada kudirin gwamnatin Tinubu na kare martabar sarakunan gargajiya a ƙasar nan.

“Ku ne masu riƙe da al’adun mu; ku ne ginshiƙan al’umma. Muna girmama ku kuma muna yaba muku domin ku ne mafi kusa da jama’a,” inji Shettima.

A nasa martanin, Lamiɗon Adamawa ya yaba da jagorancin Shugaba Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima wajen bunƙasa ƙasa.

Shettima da Fintiri da sauran manyan baƙi tare da Lamiɗon Adamawa
Tags: AdamawaAPCFintiriKashimShettimaLamiɗonAdamawasauya sheƙazaben2027
Previous Post

Nijeriya ta ƙara ƙarfafa hulɗa da Tarayyar Turai kan tsaro

Next Post

Tinubu yana murɗe wuyan dimokiraɗiyya — Nijeriya na gangarawa zuwa mulkin kama-karya – Atiku

Related Posts

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Rikicin shugabanci a ADC: Ɓangaren David Mark ya rubuta wa CJN takarda, ya roƙi a gaggauta yanke hukunci
Siyasa

Rikicin shugabanci a ADC: Ɓangaren David Mark ya rubuta wa CJN takarda, ya roƙi a gaggauta yanke hukunci

April 28, 2026
A taron Ibadan, ‘yan adawa sun haɗa kai, sun amince da tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya a zaɓen 2027
Siyasa

A taron Ibadan, ‘yan adawa sun haɗa kai, sun amince da tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya a zaɓen 2027

April 25, 2026
Next Post
Ba cewa na yi na daina takara ba, inji Atiku kan hirar sa da BBC Hausa

Tinubu yana murɗe wuyan dimokiraɗiyya — Nijeriya na gangarawa zuwa mulkin kama-karya – Atiku

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!