Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma fitaccen jigo a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya yi gargaɗi mai tsanani cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana rushe dimokiraɗiyya a zahiri tare da tura Nijeriya zuwa cikakken mulkin kama-karya, lamarin da ke da haɗari ga duk yankin Afrika ta Yamma.
A wata kakkausar suka da ya yi a ranar Litinin, Atiku ya mayar da martani kan abin da ya bayyana a matsayin ƙawanya da jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) suka yi wa gidaje da harkokin kasuwancin tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami—matakin da ya kira rashin bin doka, na ramuwar gayya, kuma na siyasa.
A sanarwar da ofishin sa na yaɗa labarai suka fitar, Atiku ya ce jami’an DSS sun mamaye tare da kulle kadarorin Malami jim kaɗan bayan ziyarar sa—duk da cewa batun yana gaban kotu.
Ya ce: “Wannan ba shugabanci ba ne. Wannan tsoratarwa ce. Wannan gwamnati ce da ke amfani da ikon hukuma don murƙushe masu adawa.”
Atiku ya yi gargaɗin cewa Nijeriya tana fuskantar rushewar ƙa’idojin dimokiraɗiyya cikin sauri a ƙarƙashin Tinubu, inda cibiyoyin gwamnati suka koma kayan aikin tsangwama na siyasa.
“Abin da muke gani shi ne bayyanannen cin zarafin iko—ana amfani da hukumomin tsaro ba don kare ƙasa ba, sai don biyan buƙatun siyasa. Ta haka ne dimokiraɗiyya ke mutuwa,” inji shi.
Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da gudanar da wani tsari na musamman domin murƙushe muryoyin adawa tare da kafa cikakken iko na siyasa gabanin zaɓen 2027.
“A fayyace a sarari: wannan gwamnati tana tsoron fafatawa. Shi ya sa take komawa amfani da ƙarfi—tsangwama, tsoratarwa, da ƙoƙarin karya gwiwar shugabannin adawa har su miƙa wuya,” inji shi.
Ya ƙara da cewa ci gaba da tsananta wa mutane irin su Nasir El-Rufa’i da Abubakar Malami wani ɓangare ne na wata babbar manufa ta tilasta musu barin siyasar adawa su koma sahun jam’iyya mai mulki ta APC.
“Wannan cin zarafin siyasa ne a mafi girman matsayi—ko ku zo mu tafi tare ko a lalata ku. Wannan ne saƙon da ake aikawa,” inji Atiku.







