Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Juma’a ya tabbatar wa ’yan Nijeriya da Sojojin Nijeriya cewa ƙasar nan za ta yi nasara a ƙarshe a kan dukkan nau’o’in rashin tsaro, yana mai jaddada cewa sadaukarwar jaruman sojojin ƙasar nan ba za ta tafi a banza ba.
Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa Tinubu ya bayar da wannan tabbacin ne yayin wani taron buɗe-baki na haɗin addinai da ya yi da shugabannin rundunonin sojojin Nijeriya a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Shugaba ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin sa na kula da jin daɗin jami’ai da sojojin da ke bakin aiki a fagen daga.
Ya ce: “Na saurari Babban Hafsan Sojin Ƙasa kan sababbin amincewar buƙatu da na bayar ga Sojojin Nijeriya.
“Aiki na shi ne in gode muku gaba ɗaya a madadin ƙasa mai godiya, domin na san cewa sau da dama kuna daɗewa ba ku tare da iyalan ku kuma kuna kasancewa nesa da su. Wasu daga cikin ku kuma na fuskantar hare-haren ’yan bindiga da ’yan ta’adda.
“Ina yaba da jarumtar ku, sadaukarwar ku da ƙwarewar ku yayin da kuke sadaukar da rayuwar ku wajen kare ’yancin kan Nijeriya da kuma tsaron jama’ar ta.”

Ya bayyana cewa ƙoƙarin dakarun na jami’an tsaro ya ci gaba da rage ƙarfin ƙungiyoyin ’yan ta’adda da ’yan bindiga da ke aiki a sassa daban-daban na ƙasar.
Ya ce: “Kun kasance kuna aiki tuƙuru wajen yi wa ƙasa hidima da kuma kare ’yancin kan mu. Wannan ƙasa za ta ci gaba da gode muku, kuma sadaukarwar ku ba za ta tafi a banza ba, ina ba ku tabbacin haka.”
Shugaban ƙasar ya kuma tabbatar musu da cewa gwamnati za ta ci gaba da saka jari wajen samar da kayan aiki na zamani, bayanan sirri da kayan tallafi na aiki domin ƙara inganta ayyukan su a fagen aiki.

Tinubu ya gode wa ’yan Nijeriya kan juriyar da suke yi a lokacin da ake sake fasalin tattalin arzikin ƙasar nan, inda ya ƙara da cewa: “Na yi farin cikin sanar da ku cewa sadaukarwar ku da ta sauran ’yan ƙasa ba ta tafi a banza ba. Yanzu mun fara fita daga cikin duhun ramin da muke ciki.”
Har ila yau, ya yi amfani da damar wajen miƙa ta’aziyyar sa ga gwamnatin da al’ummar Jihar Borno kan harin ta’addanci da ya faru kwanan nan a jihar.
Tun da farko, Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Oluwafemi Oluyode, wanda Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya wakilta, ya yaba wa Shugaban Ƙasa kan amincewar buƙatu daban-daban da ya bayar waɗanda suka inganta jin daɗin sojoji da kuma ƙwarewar ayyukan su.
Ya ce: “Ina so in gode wa Babban Kwamandan Sojojin Nijeriya bisa wannan dama ta musamman da aka samu na gudanar da buɗe-baki ga mabiya addinai biyu. Wannan lokaci na musamman yana ba mu damar sabunta hidimar mu da kuma ƙudirin mu ga ƙasar mu.
“Ina matuƙar gode wa Shugaban Ƙasar mu mai jajircewa kan amincewar buƙatu daban-daban da ya bayar, ciki har da ƙarin albashin sojojin Nijeriya da kuma ƙarin alawus na Brigade of Guards.
“Waɗannan amincewar buƙatun sun shafi samar da kayan aikin soja da kuma gina ingantattun gidaje ga sojojin ƙasar nan.
“Waɗannan matakai masu kyau za su taimaka matuƙa wajen inganta ƙwarewar ayyukan mu, kuma ina tabbatar muku cewa dukkan sojojin ƙasar nan sun karɓe su da farin ciki.”







