Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da wani kwamitin mutane 11 da zai jagoranci kafa kamfanin Grid Asset Management Company Limited (GAMCO), wani shiri da gwamnati ke ganin zai taimaka wajen magance matsalolin da suka addabi ɓangaren wutar lantarki.
Kafa kwamitin ta biyo bayan amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a zaman ta na ranar Laraba kan kafa kamfanin domin inganta sarrafa tsarin wutar lantarki da kuma rage matsalar wutar da ke yawan lalacewa.
Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, wanda ya ƙaddamar da kwamitin a madadin Shugaban Ƙasa a ranar Juma’a, ya bayyana cewa kafa GAMCO yana daga cikin manyan matakan sauyi da gwamnatin Tinubu ke ɗauka domin farfaɗo da ɓangaren wutar lantarki.
Ya ce manufar ita ce inganta samar da wuta, musamman a ɓangaren ‘grid’ da tsarin isar da wuta, tare da tabbatar da cewa Nijeriya ta amfana da dukkan ƙarfin wutar da take da shi.
A cewar sa, kwamitin zai duba dokoki, ƙa’idoji da manufofin da ke tafiyar da samar da wutar lantarki daga samarwa zuwa rarrabawa da kuma kasuwar wutar lantarki.
Haka kuma zai nazarci tasirin dokokin gyaran ɓangaren wutar lantarki na 2025, tare da gano duk wani saɓani ko tangarɗa da ka iya tasowa tsakanin tsarin GAMCO da dokoki da ƙa’idojin da ake da su a yanzu.
Kwamitin zai kuma binciki matsayin kadarori da yarjejeniyoyin Niger Delta Power Holding Company (NDPHC) da kuma ayyukan National Integrated Power Project (NIPP), musamman tashoshin wutar lantarki na Omotosho, Olorunshogo da Ihovbor, waɗanda za su kasance matakin farko na aikin kamfanin.
Bugu da ƙari, za su duba alaƙar ayyukan GAMCO da nauyin da dokar ta ɗora wa Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC), tare da nazarin tasirin kuɗi da kasuwa, ciki har da batun tallafin gwamnati da kuɗaɗen shiga.
Kwamitin yana ƙarƙashin jagorancin Femi Gbajabiamila a matsayin shugaba, yayin da Ministan Shari’a, da ministocin Wuta, Ayyuka, da Kuɗi suke membobi.
Sauran sun haɗa da ministocin Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, Sufurin Jiragen Sama, Ƙaramin Ministan Man Fetur, Shugaban Hukumar Haraji ta Nijeriya, da kuma masani a fannin makamashi Farfesa Yemi Oke.
Dakta John Chidiebere Ezeamama, sakataren ma’aikatar harkokin Majalisar Zartarwa, shi ne sakataren kwamitin.
Sabon kamfanin GAMCO zai mayar da hankali kan farfaɗo da wutar da ke maƙale a tsarin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hanyar wutar Benin zuwa Legas a matsayin matakin gwaji.
Gwamnati na sa ran kamfanin zai iya dawo da aƙalla megawatt 1,600 na wuta cikin watanni 18 zuwa 24, tare da gina sabuwar babbar tashar wutar lantarki mai ƙarfin 330KV a wannan yankin.
Gwamnatin Tarayya ce za ta mallaki kamfanin gaba ɗaya ta hannun Ma’aikatar Kuɗi (Ministry of Finance Incorporated), yayin da ake sa ran nasarar matakin gwajin zai zama tubalin faɗaɗa tsarin zuwa sauran yankuna na ƙasar nan domin tabbatar da daidaiton wutar lantarki, ƙarfafa masana’antu, jawo zuba jari da kuma inganta rayuwar al’ummar Nijeriya, daidai da manufofin Renewed Hope Agenda na gwamnatin Tinubu.






