Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana takamaiman yawan bankuna 30 cewa sun rigaya sun cika sabbin ƙa’idojin mafi ƙarancin jarin da ake buƙata bisa irin lasisin da kowannen su yake da shi.
CBN ya ce a ranar 6 ga Maris, 2026 aka samu yawan wannan adadin bankunan.
CBN ya kuma bayyana cewa gaba ɗaya bankuna 33 sun samu ƙarin jari ta hanyoyi daban-daban da CBN ya gindaya bisa doka, a matsayin wani ɓangare na shirin sake ƙarfafa jarin bankuna da ake aiwatarwa.
A cikin wata sanarwa wadda Daraktar Sadarwa ta CBN, Hakama Sidi Ali, ta ce matsayin jarin sauran bankunan da suka rage yana cikin tsarin tantancewa na yau da kullum da bankin ke yi kafin a tabbatar da cikakken bin ƙa’idojin a cikin wa’adin shirin ƙara ƙarfin jari.
Ta bayyana cewa CBN ya ƙaddamar da shirin sake ƙarfafa jarin bankuna a shekarar 2024 domin ƙarfafa juriyar tsarin banki, tabbatar da daidaito da kuma ƙarfafa ƙarfin tsarin kuɗi na ƙasar nan, domin tallafa wa ci gaban tattalin arzikin Nijeriya.
Hajiya Hakama ta ƙara da cewa tun bayan ƙaddamar da wannan tsari, bankuna a faɗin ƙasar sun ɗauki matakai domin ƙarfafa jarin su bisa sabbin ƙa’idojin da aka gindaya. Ta kuma jaddada cewa aikin ƙara jarin bankuna na tafiya yadda ya kamata.
CBN ya sake jaddada cewa tsarin banki na Nijeriya yana nan cikin ƙarfi da kwanciyar hankali.
Sanarwar ta ƙara da cewa: “Shirin ƙara jarin bankuna yana tafiya yadda aka tsara kuma zai ƙara ƙarfafa ƙarfin bankunan Nijeriya wajen tallafa wa iyalai, ‘yan kasuwa da kuma ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.
“CBN za ta ci gaba da sanya ido sosai kan bankunan da take kula da su domin tabbatar da cikakken bin ƙa’idojin kula da harkokin banki da kuma ƙa’idojin jarin bankuna.”
A ƙarƙashin jagorancin Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, bankin ya sanar a ranar 28 ga Maris, 2024 da shirin sake ƙarfafa jarin bankuna na tsawon shekaru biyu, wanda ya fara aiki daga 1 ga Afrilu, 2024.
Wa’adin cikar wannan shiri na watanni 24 zai ƙare a ranar 31 ga Maris, 2026.
Ana sa ran ƙarin jarin da aka buƙata zai taimaka wajen tabbatar da cewa bankunan Nijeriya suna da ƙarfin ɗaukar manyan ƙalubale da ke tattare da hada-hadar kuɗi, tare da tsayawa da ƙarfi a lokacin matsalolin tattalin arziki na cikin gida da na ƙasashen waje.
Haka kuma zai ƙara yawan kuɗin da bankuna ke da shi, wanda zai ƙara musu ƙarfin jure asara,
musamman, sabon tsarin ya tanadi cewa:
Bankunan kasuwanci masu lasisin ƙasa da ƙasa (international licence) dole su mallaki aƙalla Naira biliyan 500 a matsayin jari.
Bankunan kasuwanci masu lasisin ƙasa (national licence) su kuma tilas su mallaki aƙalla Naira biliyan 200.
Bankunan kasuwanci masu lasisin yanki (regional licence) su mallaki aƙalla Naira biliyan 50.
Kafin sanar da waɗannan sabbin ƙa’idojin, bankuna da dama suna aiki ne da ƙaramin jari duk da irin ribar da suke samu, idan aka kwatanta da bankunan ƙasashen Afrika.
Misali, a baya bankunan kasuwanci masu lasisin ƙasa da ƙasa ana buƙatar su riƙe jari mafi ƙaranci na Naira biliyan 25 kacal.







