• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Garaɓasa: Majalisar Zartarwa ta amince da ba ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da za su yi ritaya giratuti na ƙunshin albashin shekara guda

ALI KANO by ALI KANO
March 5, 2026
in Labarai
A A
0
Garaɓasa: Majalisar Zartarwa ta amince da ba ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da za su yi ritaya giratuti na ƙunshin albashin shekara guda
Misis Esther Didi Walson-Jack (Hoto: Patient Olumati/Radio Nigeria)

Misis Esther Didi Walson-Jack (Hoto: Patient Olumati/Radio Nigeria)

Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da aiwatar da wani sabon shiri na Exit Benefit Scheme, wanda zai bai wa ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da suka yi ritaya giratuti da ya kai kashi 100 cikin 100 na jimillar albashin su na shekara guda.

Shirin, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026, ana sa ran zai inganta matuƙa fa’idodin ritaya ga jami’an da suka yi wa ƙasa hidima na aƙalla shekaru 10 a aikin Gwamnatin Tarayya.

Tsarin yana daga cikin muhimman sauye-sauyen jin daɗin ma’aikatan gwamnati a ‘yan shekarun nan, kuma yana nuna ƙoƙarin gwamnati na tabbatar da cewa ma’aikatan gwamnati suna yin ritaya tare da ingantaccen tsaro na kuɗi.

An bayyana wannan cigaba ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a a Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Eno Olotu, ya sanya wa hannu.

A cewar sanarwar, sabon tsarin zai bai wa ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da za su yi ritaya giratuti da ya yi daidai da jimillar dukkan albashin da suke samu na shekara guda.

An tsara wannan manufa ne domin ƙarfafa tsarin jin daɗin ma’aikatan gwamnati tare da samar musu da ƙarin kariya ta kuɗi a ƙarshen aikin su.

Jami’ai sun bayyana cewa shirin zai shafi ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da ke aiki a ma’aikatun da baitulmali ke ɗaukar nauyin su, sassan gwamnati masu zaman kan su daga ma’aikatu (extra-ministerial departments), da kuma hukumomin gwamnati.

Amincewar ta biyo bayan tattaunawa da shawarwari da aka shafe watannin ana yi da wani Kwamitin Fasaha na Ma’aikatun Gwamnati da dama (Inter-Ministerial Technical Committee) da Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ya kafa.

Kwamitin ya yi aiki tare da wasu cibiyoyin gwamnati da dama, ciki har da Hukumar Kula da Fansho ta Ƙasa, Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya, da kuma Ofishin Akanta Janar na Tarayya.

Waɗannan hukumomi sun haɗa kai wajen samar da tsarin da zai tabbatar da cewa shirin mai ɗorewa ne, tare da ba da gagarumin tallafin kuɗi ga ma’aikatan da za su yi ritaya.

Jami’an gwamnati sun bayyana cewa Exit Benefit Scheme ba zai maye gurbin tsarin fansho na yanzu ba, sai dai ƙarin inganta tsarin Contributory Pension Scheme da aka fara a shekarar 2004.

A ƙarƙashin sabon tsarin, ma’aikatan gwamnati da suka cancanta za su karɓi giratuti ɗin tare da kuɗin fansho, wanda hakan zai ƙara inganta dukkan ƙunshin fa’idodin ritayar su.

Ana sa ran wannan shiri zai samar da ingantaccen tsaro na samun kuɗin shiga ga tsofaffin ma’aikatan gwamnati, tare da rage rashin tabbas na kuɗi bayan sun bar aikin gwamnati.

Da take mayar da martani kan wannan hukunci, Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Walson-Jack, ta bayyana amincewar a matsayin babban muhimmin mataki a tarihin aikin gwamnati a Nijeriya.

Ta ce wannan manufa na nuna ƙudirin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na girmama sadaukarwa da jajircewar ma’aikatan gwamnati.

Ta ce: “Wannan amincewa wata babbar shaida ce ta yadda gwamnati ke daraja gagarumar gudunmawar ma’aikatan gwamnati, waɗanda suka sadaukar da shekarun su mafi ƙwazo wajen yi wa jama’a hidima da kuma cigaban ƙasa.”

Walson-Jack ta ƙara da cewa shirin zai inganta fa’idojin ritaya sosai, tare da ƙara ƙarfafa amincewar ma’aikata ga ƙudirin gwamnati na kula da jin daɗin su.

A cewar ta, manufar ta kuma yi daidai da gyare-gyaren da ake yi yanzu domin gina aikin gwamnati da ya fi inganci, kuzari, kuma mai mayar da hankali kan sakamako.

Ta tabbatar da cewa cikakkun ƙa’idojin yadda za a aiwatar da shirin za a sanar da su ga ma’aikatu da hukumomin da abin ya shafa nan gaba.

Wannan cigaba ya fi ɗaukar hankali musamman saboda ya zo shekaru 22 bayan ƙaddamar da tsarin fansho na Contributory Pension Scheme, wanda a wancan lokacin ya maye gurbin tsohon tsarin giratuti.

Sabuwar amincewar da Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta bayar yana nuna sabon yunƙuri na Gwamnatin Tarayya wajen inganta jin daɗin ma’aikatan ta, tare da ƙarfafa sauye-sauyen da za su tabbatar da makomar aikin gwamnati a Nijeriya.

Tags: AikinGwamnatialbashiEstherDidiWalsonJackFECgiratutiMajalisarZartarwaritaya
Previous Post

Haske daga CBN: Alamomi masu nuna Nijeriya ta shiga 2026 da ƙafar dama

Next Post

Nijeriya za ta yi ƙarin sojoji 28,000 cikin shekara guda — COAS

Related Posts

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500
Labarai

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

May 13, 2026
Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Next Post
Nijeriya za ta yi ƙarin sojoji 28,000 cikin shekara guda — COAS

Nijeriya za ta yi ƙarin sojoji 28,000 cikin shekara guda — COAS

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!