Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya (NPF) ta ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke iƙirarin cewa wani bidiyo da ya karaɗe intanet ya nuna wani jami’in ɗan sanda yana jinjina wa ‘yan bindiga a Jihar Katsina.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, CSP Anietie Okokon Edem Iniedu, ya fitar a yau Laraba, rundunar ta bayyana cewa mutanen da ke ɗauke da makamai da aka gani a cikin bidiyon ba ‘yan bindiga ba ne, illa mambobi ne da aka amince da su na Ƙungiyar ‘Yan Banga ta Nijeriya (Vigilante Group of Nigeria – VGN) da kuma mafarauta masu rijista da ke aiki tare da hukumomin tsaro.
Sanarwar ta ce waɗannan jami’an tsaron al’umma suna taimaka wa hukumomin tsaro wajen gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro a Ƙananan Hukumomin Musawa da Matazu na Jihar Katsina.
Rundunar ta bayyana cewa bidiyon ya ɗauki wani yanayi ne na yau da kullum inda wani jami’in ɗan sanda ke mu’amala da waɗannan masu aikin sa-kai yayin da suke kan hanyar su ta zuwa wani wurin gudanar da aiki domin tallafa wa ƙoƙarin yaƙi da miyagun laifuka da kuma tabbatar da tsaron al’umma.
Ta bayyana cewa duk wani iƙirarin da ke cewa jami’in ɗan sandan yana hulɗa da ‘yan bindiga ƙarya ce tsagwaron ta, mai cike da muguwar manufa, wadda aka ƙirƙira domin yaudarar jama’a.
Rundunar ta yi Allah-wadai da karkatar da gaskiya da kuma yaɗa bayanan ƙarya da ka iya haddasa fargaba a tsakanin jama’a, rage amincewa da hukumomin tsaro, tare da kawo cikas ga ayyukan tabbatar da tsaro.
Ta buƙaci jama’a da su yi watsi da iƙirarin da ake yaɗawa tare da bidiyon, tare da dogaro da bayanan da hukumomin ‘yan sanda da sauran hukumomin gwamnati da aka amince da su suke fitarwa.
Har ila yau, rundunar ta gargaɗi duk masu kicker’s ko yaɗa bayanan ƙarya da za su iya kawo barazana ga zaman lafiya da tsaro da su daina hakan, tana mai jaddada cewa za a ɗauki matakin doka kan duk wanda aka samu da laifi.
Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta sake tabbatar da ƙudirin ta na ci gaba da haɗa gwiwa da halastattun ƙungiyoyin tsaron al’umma da sauran abokan hulɗa domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma yaƙi da aikata laifuka a faɗin ƙasar nan.






