Mai Martaba Sarkin Kano, Dakta Muhammadu Sanusi II, zai yi bikin naɗin tsohon Hafsan Sojin Saman Nijeriya, Mohammad Dikko Umar, a matsayin Sarkin Fulanin Ja’idanawa a ranar Juma’a.
Sarkin Kano ya bayyana naɗin Dikko Umar a watan Afrilu, bayan rasuwar Abubakar Buhari, wanda shi ne yake riƙe da wannan sarauta kafin rasuwar sa.
Sarautar Sarkin Fulanin Ja’idanawa tana daga cikin manyan sarautun gargajiya a Masarautar Kano, kuma tana ƙarƙashin ikon Mai Martaba Sarkin Kano.







