Wasu masallata sun rasa rayukan su, yayin da wasu kuma suka jikkata, a yammacin jiya Laraba lokacin da bam ya fashe yayin sallar Magariba a wani masallaci da ke Kasuwar Gamborun a Maiduguri.
DSP Nahum Daso, kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Borno, ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Maiduguri.
Daso ya ce ana zargin wani ɗan ƙunar baƙin wake ne ya tayar da bam ɗin da misalin ƙarfe 6:15 na yamma, a lokacin da wasu Musulmai ke gudanar da sallar jam’i.
“Binciken farko ya nuna cewa fashewar ta samo asali ne daga wani ɗan ƙunar baƙin wake da ya kai harin yayin sallar Magariba,” inji shi.
A cewar sa, fashewar ta kashe wasu da ke sallah nan take, yayin da ta bar da dama da raunuka daban-daban.
Ya ce an gaggauta kwashe waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri domin samun kulawar lafiya.
Kakakin ya bayyana cewa jami’an sashen kawar da bama-bamai tare da sauran hukumomin tsaro sun isa wajen domin tabbatar da tsaro da kuma kawar da yiwuwar kasancewar wasu abubuwan fashewa.
Daso ya ƙara da cewa an killace yankin, yayin da wata ƙungiya ta haɗin gwiwar hukumomin tsaro ta fara cikakken bincike domin gano yadda harin ya faru da kuma waɗanda ke da hannu a kai.
Ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalin su tare da kasancewa masu sa ido, su kuma gaggauta kai rahoton duk wani motsi ko mutum da ake zargi ga hukumomin tsaro.
Kasuwar Gamborun na ɗaya daga cikin kasuwanni mafi cunkoso a Maiduguri, kuma yawanci tana cika da jama’a musamman a lokacin sallar magariba.







