• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Trump ya amince ana kashe Musulmi a Nalijeriya, ya yi ishara da yiwuwar ƙarin hare-haren Amurka

Wakilin Mu by Wakilin Mu
January 9, 2026
in Tsaro
A A
0
Trump ya amince ana kashe Musulmi a Nalijeriya, ya yi ishara da yiwuwar ƙarin hare-haren Amurka
Shugaba Donald Trump

Shugaba Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya amince cewa ana kashe Musulmi ma a Nijeriya, amma ya jaddada cewa Kiristoci ne ke kasancewa manyan waɗanda ake kai wa hare-haren tashin hankali, tare da gargaɗin cewa Amurka na iya kai ƙarin hare-haren soji idan irin wannan tashin hankalin ya ci gaba.

Trump ya yi waɗannan kalamai ne a wata hira da jaridar The New York Times da aka wallafa a ranar Alhamis, yayin da yake amsa tambayoyi kan wani harin sojin Amurka da aka kai a ranar Kirsimeti a Nijeriya.

Sojojin Amurka sun ce harin ya nufi ‘yan ƙungiyar Islamic State (ISIS) ne a arewa-maso-yammacin Nijeriya, kuma an gudanar da shi ne bisa buƙatar gwamnatin Nijeriya. Amma hukumomin Nijeriya sun bayyana lamarin a matsayin “aikin haɗin gwiwa” kan “’yan ta’adda,” suna jaddada cewa ba a kai harin ne kan wata ƙungiya ta addini ta musamman ba.

“Ina so ya zama hari na lokaci guda,” inji Trump. “Amma idan suka ci gaba da kashe Kiristoci, to zai zama hare-hare masu yawa.”

Da aka tambaye shi ya mayar da martani ga kalaman mai ba shi shawara kan harkokin Afrika cewa ‘yan ISIS da Boko Haram suna kashe Musulmi fiye da Kiristoci, sai Trump ya ce: “Ina ganin ana kashe Musulmi ma a Najeriya. Amma mafi yawanci Kiristoci ne.”

A ƙarshen watan Oktoba, Trump ya fara gargaɗi a bainar jama’a cewa Kiristanci na fuskantar abin da ya kira “barazanar wanzuwa” a Nijeriya, yana zargin gwamnatin Nijeriya da gaza kare al’ummomin Kiristoci yadda ya kamata, tare da barazanar sojin Amurka za su sa hannu.

Nijeriya, ƙasa mafi yawan jama’a a Afrika wadda ke da sama da mutane miliyan 230, kusan rabi-rabi ce tsakanin Kiristoci, waɗanda galibi suke a kudu, da Musulmi, waɗanda suka fi yawa a arewa.

Duk da ƙalubalen tsaro da ke ci gaba da addabar ƙasar, ciki har da tashe-tashen hankula na ‘yan tawaye, ‘yan bindiga da sace-sace, hukumomin Nijeriya sun sha yin watsi da iƙirarin cewa ana zaluntar Kiristoci da gangan. Gwamnatin ta jaddada cewa hare-haren ‘yan tawaye sun hallaka Musulmi da Kiristoci baki ɗaya.

Duk da cewa Nijeriya ta nuna shirin ta na haɗa kai da Amurka wajen yaƙi da ƙungiyoyin ‘yan tada ƙayar baya, ta nuna adawa sosai da ra’ayoyin da ke nuna cewa tashin hankalin a ƙasar na shafar Kiristoci kaɗai ne.

(Reuters)

Tags: Donald Trumpharikashe-kasheKiristocisojoji
Previous Post

Tinubu ya yaba wa Kasuwar Hannun Jari ta Nijeriya bisa kaiwa darajar naira tiriliyan 100

Next Post

Gwamnatin Tarayya da ta Neja sun rattaba hannu kan yarjejeniyar shirin bunƙasa tattalin arzikin jama’a

Related Posts

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma
Tsaro

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma

April 25, 2026
Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos
Tsaro

Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos

April 17, 2026
‘Yan sanda sun miƙa wani da ake zargi da kisan kai ga hukumomin Birtaniya
Tsaro

‘Yan sanda sun miƙa wani da ake zargi da kisan kai ga hukumomin Birtaniya

April 16, 2026
Sojoji sun ragargaji maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su
Tsaro

Sojoji sun ragargaji maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su

April 15, 2026
Nijeriya ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba – Gwamnatin Tarayya
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta kare harin jirgin sama a Jilli, ta ba da umurnin bincike

April 14, 2026
An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno
Tsaro

An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno

April 13, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya da ta Neja sun rattaba hannu kan yarjejeniyar shirin bunƙasa tattalin arzikin jama’a

Gwamnatin Tarayya da ta Neja sun rattaba hannu kan yarjejeniyar shirin bunƙasa tattalin arzikin jama'a

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!