• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya yaba wa Kasuwar Hannun Jari ta Nijeriya bisa kaiwa darajar naira tiriliyan 100

Wakilin Mu by Wakilin Mu
January 8, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Tsaro: Tinubu ya kira taron Majalisar Ƙoli ta ƙasa da ta ‘yan sanda
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa kamfanonin Nijeriya, jama’ar ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki a kasuwar hannun jari bisa nasarar da Kasuwar Musayar Hannun Jari ta Nijeriya (NGX) ta kai darajar kasuwa ta naira tiriliyan 100.

A cikin wata sanarwar fadar shugaban ƙasa da mai ba shi shawara na musamman kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, Tinubu ya ce wannan gagarumar nasarar ta zama abin ƙarfafa gwiwa ga masu zuba jari a kasuwannin kuɗi da jarin ƙasa.

Shugaban ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su zuba jari a tattalin arzikin cikin gida, yana mai tabbatar da cewa shekarar 2026 za ta kawo riba mafi yawa yayin da gyare-gyaren tattalin arzikin gwamnatin sa ke ƙara haifar da sakamako mai ƙarfi.

Tinubu ya ce hayewar kasuwar Musayar Hannayen Jari ta Nijeriya (NGX) zuwa darajar naira tiriliyan 100 alama ce ta sabon yanayin tattalin arziki da farfaɗo da kasuwar Nijeriya.

Ya bayyana cewa a 2025, duk da cikas da wasu kasuwannin duniya suka fuskanta, Alamar All-Share ta NGX ta tashi da kaso 51.19 cikin 100, fiye da kaso 37.65 na shekarar 2024, lamarin da ya sanya Nijeriya cikin manyan kasuwanni masu riba a duniya.

Ya ƙara da cewa ribar da aka samu a bana ta zarce ta manyan kasuwannin duniya kamar S&P 500 da FTSE 100, har ma da wasu kasuwannin ƙasashe masu tasowa na ƙungiyar BRICS+, yana mai cewa Nijeriya ba ƙasar da za a yi watsi da ita ba ce, illa wata ƙasa da ake gano ƙima a cikin ta.

Shugaban ya nuna cewa kamfanoni da dama a dukkan fannoni sun nuna ƙwazo a NGX, daga manyan masana’antu da suka ƙarfafa samarwa a gida, zuwa bankuna da suka nuna juriya da ƙirƙira ta fasaha.

Ya ce hakan na tabbatar da cewa kamfanonin Nijeriya na iya samar da riba mai kyau ga masu zuba jari.

Tinubu ya kuma bayyana cewa ana sa ran ƙarin kamfanoni, musamman na makamashi, fasaha, sadarwa da manyan ayyukan more rayuwa, za su shiga kasuwar hannun jari, abin da zai ƙara darajar kasuwa da faɗaɗa mallakar tattalin arziki ga jama’a.

Game da gyare-gyaren tattalin arziki, shugaban ya ce bayan ƙalubalen farko, ana ganin saukar hauhawar farashi sakamakon tsauraran matakan kuɗi da dakatar da biyan “Ways and Means”, tare da bunƙasar zuba jari a noma.

Ya ce hauhawar farashi ta ragu daga kashi 34.8 cikin 100 a Disamba 2024 zuwa kashi 14.45 cikin 100 a Nuwamba 2025, kuma ana hasashen ta kai kashi 12 a 2026, har ma ta faɗi ƙasa da kashi 10 kafin ƙarshen shekarar.

Tinubu ya ce ma’aunin asusun kasuwanci na ƙasa ya nuna ingantaccen yanayi, inda Nijeriya ta samu rarar dala biliyan 16 a 2024, tare da hasashen kaiwa dala biliyan 18.81 a 2026.

Ya ƙara da cewa fitar da kayayyakin da ba na mai ba ya ƙaru da kashi 48 zuwa naira tiriliyan 9.2 a zangon uku na 2025, yayin da fitarwa zuwa Afrika ya tashi da kashi 97.

Shugaban ya kuma nuna cewa ajiyar kuɗaɗen waje ya wuce dala biliyan 45, tare da hasashen kaiwa dala biliyan 50 a farkon zangon 2026, yayin da naira ta samu daidaito.

Ya ambaci ci gaba a hanyoyin jirgin ƙasa, manyan tituna, tashoshin jiragen ruwa, da kuma manyan ayyukan superhighway na Legos–Kalaba da kuma Sokoto–Badagiri.

A cewar Tinubu, ana samun inganci a cibiyoyin kiwon lafiya, raguwar kuɗin yawon neman magani a ƙasashen waje, tallafin lamunin ilimi na NELFUND, da ƙarin tallafin bincike ga jami’o’i.

Ya kammala da cewa gina ƙasa tsari ne mai ɗaukar lokaci, inda naira tiriliyan 100 ta zama saƙo ga duniya cewa tattalin arzikin Nijeriya na da ƙarfi.

Ya yi alƙawarin ci gaba da aiki tuƙuru wajen gina tattalin arziki mai daidaito, gaskiya da bunƙasa, tare da aiwatar da manyan gyare-gyaren haraji da kuɗi da suka fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026.

Tags: Bola Ahmed Tinubukasuwar hannun jariNGX
Previous Post

Kotu ta ba Malami, matar sa da ɗan sa belin N500m kowannen su

Next Post

Trump ya amince ana kashe Musulmi a Nalijeriya, ya yi ishara da yiwuwar ƙarin hare-haren Amurka

Related Posts

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai

May 12, 2026
Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis

May 12, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙwaƙudumar kasa biyan tulin bashin da manyan bankuna suka bayar laifin daraktoci da manyan masu hannayen jarin su ne, ba laifin CBN ba

May 8, 2026
Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya

May 7, 2026
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda ƙarfin laƙani da dafa’in CBN ke hana girgizar tattalin arzikin duniya yi wa Nijeriya barazana

May 6, 2026
Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris

May 5, 2026
Next Post
Trump ya amince ana kashe Musulmi a Nalijeriya, ya yi ishara da yiwuwar ƙarin hare-haren Amurka

Trump ya amince ana kashe Musulmi a Nalijeriya, ya yi ishara da yiwuwar ƙarin hare-haren Amurka

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!